CORONA: Gwamnati Ta Ƙara Mako Guda Na Dokar Hana Walwala

Gwamnatin tarayya ta kara mako daya bisa tsarin babi na biyu na sassauta dokar hana walwala a kasar nan.

Sakataren gwamnati kuma shugaban kwamitin shugaban kasa kan dakile yaduwar cutar Covid-19 Boss Mustapha ya sanar da haka a Abuja ranar Litini.

Ya ce mako dayan da gwamnati ta kara zai fara ranar 29 ga watan Yuli zuwa 6 ga watan Agusta.

Mustapha ya ce za a ci gaba da sassauta tsarin dokar hana walwala da gwamnati ta saka a babi na biyu a cikin karin mako daya din da gwamnati ta yi.

Ya ce gwamnati ta ii wanna karin ne domin kare kiwon lafiyar mutane daga cutar Korona a wannan lokaci da ake tunkarar bukukuwan Babban Sallah.

Annobar Korona a Najeriya

Sakamakon binciken da hukumar NCDC ta fitar ranar Lahadi ya Nina cewa Najeriya ta Sami Karin Mutum 555 da Suka kami da cutar.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum -156, Kano 65, Ogun 57, Filato 54, Oyo 53, Benue 43, FCT 30, Ondo 18, Kaduna 16, Akwa Ibom 13, Gombe 13, Rivers 12, Ekiti 9, Osun 8, Cross River 3, Borno 2, Edo 2, Bayelsa 1

Yanzu mutum 40,532 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 17,374 sun warke, 858 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 22,300 ke dauke da cutar a Najeriya.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 14,456
FCT – 3,481,
Oyo – 2,570,
Edo – 2,167,
Delta – 1,464,
Rivers –1,652,
Kano –1,520,
Ogun – 1,301,
Kaduna – 1,365,
Katsina –733,
Ondo – 1,061 ,
Borno –611,
Gombe – 571,
Bauchi – 538,
Ebonyi – 759,
Filato – 834,
Enugu – 741,
Abia – 536,
Imo – 465,
Jigawa – 322,
Kwara – 711,
Bayelsa – 327,
Nasarawa – 308,
Osun – 443,
Sokoto – 153,
Niger – 168,
Akwa Ibom – 221,
Benue – 337,
Adamawa – 140,
Anambra – 132,
Kebbi – 90,
Zamfara – 77,
Yobe – 66,
Ekiti – 113,
Taraba- 54,
Kogi – 5, da Cross Rivers – 40.

Labarai Makamanta

Leave a Reply