CORONA: Ganduje Ya Haramta Dukkanin Wani Taro A Kano

Gwamnatin jihar Kano ta bada umarnin rufe wuraren taro da bukukuwa tare da umartar ma’aikata da su zauna a gida zuwa wani lokaci nan gaba a matsayin wani ɓangare na matakan da take dauka domin dakile yaduwar annobar korona a jihar.

Gwamnatin ta kuma haramta bude gidajen kallon kwallo da ke fadin jihar, sakamakon karuwar alkaluman masu dauke da korona da ake samu a jihar.

Kwamishinan yada labaran jahar, Malam Muhammad Garba ne ya fitar da wannan sanarwa a ranar Talatar nan, inda ya bayyana cewa gwamna Ganduje ya dauki wannan matakin ne bayan taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a ranar Litinin.

Sannan, sanarwar ta kara da cewa, “ma’aikatan da aikinsu ya zama dole ko masu aiki na musamman kamar jami’an lafiya da kashe gobara da malaman makarantu da jami’an tsaro da ‘yan jaridu kawai ne haramcin bai shafa ba”.

Gwamnatin ta kuma ce za ta ci gaba da aiki tukuru domin tabbatar da cewa kowa na mutunta ka’idoji da bin dokokin kare kai daga kamuwa da cutar ta korona.

Matakin gwamnatin na zuwa ne kwana guda da sake bude makarantu a fadin Jihar.

Labarai Makamanta