Gwamna Ahmadu Fintiri ya ce a sakamakon rashin bin dokoki da ka’idojin kariya daga cutar korona a jihar Adamawa da mutane ke yi na wanke hannuwa, sanya takunkumin fuska, bayar da tazara daga yanzu ya haramta yin taro a fadin jihar
Mista Fintiri ya ce ya rufe duka cibiyoyin shakatawa, kulub-kulub, da tarurruka.
Kazalika ya bukaci malaman Addini su tashi tsaye wajen ganin mabiyansu sun bi dokikin kariya daga cutar a wuraren ibada.
Manuniya ta ruwaito Gwamna Fintiri na cewa dokar da ya sanya a watan Maris din 2020 tana nan daram saboda haka ya baiwa jami’an tsaro dama su tabbatar ana bin dokar.
“Sannan an haramta zirga-zirga daga karfe 10 na dare zuwa karfe 5 na safiya daga nan har sai yadda hali yayi.