Shahrarren malaminan dake garin Kaduna kana kuma mataimakin shugaban majalisar malamai na kasa na kungiyar Izalah Jos, Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun ya mayarwa masu zargin Malamai da goyan bayan rufe masallatai da martani cewa “ni wallahi ban taba goyon bayan a rufe masallatai ba”
Ya ce abin takaici ne a ce Malamin addinin musulunci zai goyi bayan rufe masallaci ya ce sam bai samu wata fatawa da ta nuna a rufe masallaci ba.
Sheikh Rigachikun ya kara da cewa duk Malamin da ya goyi bayan rufe masallaci sai ya tanadi amsar da zai bawa Allah.
Har yanzu jihar Kaduna ba a bude masallatan kamsu-salawat ba duk da nasarar da ake samu wajen yaki da cutar corona a Nijeriya.