CORONA: Dubai Ta Aiko Wa Najeriya Tallafi

Firaministan Hadaddiyar Daular labarawa (Dubai) Sheikh Mohammed bin Rashid Al-Maktoum ya bada umurnin aiko da kayan tallafi zuwa Nijeriya, kuma tuni kayan suka iso.

Kayan wadanda suka hada da abinci, magani, da kuma kayan rigakafi daga kamuwa da cutar Covid-19 sun iso Nijeriya, kuma tuni aka mika su ga gwamnatin tarayya.

A jawabin Sheikh Mohammed bin Rashid Al-Maktoum ya ce “wajibin kasar Dubai ce ta taimakawa Nijeriya, kasancewar Nijeriya ita ce kasa ta farko a sahun kasashe a Nahiyar Africa masu huldayyar kasuwanci da kasar Dubai, don haka wajibin kasar Dubai ne ta taimakawa Nijeriya, musamman a irin wannan lokaci da cutar Covid-19 ta mamaye duniya”.

Muna fatan wannan tallafi zai kai ga hannun talakawa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply