Kwamitin shugaban kasa kan Covid-19 ya yi kira ga ‘yan Nijeriya subi ka’idojin da aka shinfida. Amman matukar alkalumar masu dauke da cutar sarkewar nunfashin(korona) ya cigaba da hauhawa dole ne a kulle kasar kamin a sake shawo kan annobar.
Ko a farkon shekarar data gabata na 2020, irin matakin da gwamnatin tarayya ta dauka kenan lokacin da aka samu barkewar annobar a najeriya. Wanda sauran jihohi dole suka rurrufe iyakokinsu wanda masana tattalin arzikin duniya suka bayyana wannan mataki a matsayin abin da ya kawo durkushewar tattalin arzikin kasar da duniya baki daya.
Shugaban Kwamitin Boss Mustapha ya bayyana haka a lokacin wani taron ganawa da ‘yan jaridu, ranar Litinin a babban birnin tarayya Abuja.
Mustapha wanda kuma shi ne Sakataren Gwamnatin Tarayya ya ce ‘yan kasar za su iya kaucewa haka idan har suka yi biyayya ga ka’idojin kariya daga kamuwa da cutar da gwamnati ta fitar.
Mai karatu kana ganin kulle kasar nan zai kawo karshen wannan annoba ta corona a fadin kasar mu Najeriya?