CORONA Ce Silar Karbo Bashin Najeriya – Ministar Kudi

A yayin da ake ci gaba da korafe-korafe da bayyana damuwa kan nauyin bashin da ya yi wa Najeriya katutu, gwamnatin tarayya ta yi magana kan larurorin da suke tilasta mata cin bashi.

Mun samu cewa, ministar kudi, kasafi da tsare-tsare, Zainab Ahmed, ta bayyana dalilin da ya sa kasar nan ba za ta daina ciwo bashin ba a yanzu.

Ministar ta ce a hakinanin gaskiya, annobar korona da kuma karyewar da farashin man fetur ya yi a kasuwar duniya, su ne dalilai biyu da suke tilastawa kasar nan fita neman bashi a ketare.

Ta bayyana cewa, tun gabanin bullar annobar korona wadda ta janyo karayar tattalin arziki a fadin duniya, Najeriya ta yi fama da karancin kudaden shiga lamarin da ya jefa kasar cikin mawuyancin hali.

Ministar ta zayyana cewa, wannan babban kalubale ya taka rawar gani wajen hana gwamnatin sauke wasu nauye-nauye da suka rataya wuyanta na hidimtawa al’umma.

Furucin ministar ya zo kwanan nan a wani taro ta hanyar gizo da ta halarta tare da wasu kungiyoyin daban-daban masu ruwa da tsaki kan tattalin arziki da saka hannun jari.

Ministar wacce mai ba wa shugaban kasa shawarwari na musamman kan harkokin kudi da tattalin azriki,Mrs Sarah Alade ta ce gwamnati ta na iya bakin kokarin ta don ganin ta fadada hanyoyin samar da kudaden shiga da kuma rage kashe kudi.

Jimillar bashin kudin da ake bin Najeriya ya haura Naira Tiriliyan 28.63 (N28.63tn), ofishin kula da basussukan Najeriya DMO ta alanta ranar Alhamis.

Labarai Makamanta

Leave a Reply