CORONA: Buhari Ya Janjanta Wa Trump

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika saƙon jaje da addu’o’in ga shugaban kasan Amurka, Donal Trump, da uwargidarsa, Melania Trump, da suka kamu da cutar nan mai sarke numfashi ta COVID-19.

Buhari ya aike sakonsa a jawabin da ya saki ranar Juma’a a shafinsa na Tuwita. A cewarsa, kamuwa da cutar da Trump yayi ya nuna cewa irin hadarin da cutar ke da shi ga duniya gaba daya.
“Ina yiwa shugaban kasan Amurka, Donald Trump, da uwargidarsa, Melania, samun lafiya daga cutar COVID-19.”

Shugaban kasar Amurka Donald Trump da matarsa Melania sun kamu da COVID 19 da aka fi sani da korona kimanin kwanaki 31 kafin zaben shugaban kasa na shekarar 2020 a kasar.

Shugaban kasar ya tabbatar da hakan a shafinsa na Twitter bayan daya daga cikin hadimansa Hope Hicks ya kamu da cutar tunda farko.

Labarai Makamanta

Leave a Reply