Ministan sufuri, Rotimi Amaechi yace ” babu wata fa’ida wurin dawo da zurga-zurgan sufurin jiragen kasa a halin yanzu. Ministan yace akwai hatsari mai yawa musamman idan akayi la’akari da yadda cutar covid 19 ke kara yaduwa cikin al’umma.
Amaechi yace ”Kowani tarago yana daukar mutane 88, inda koda an rage mutanen zuwa 40 domin bayar da tazara a tsakankanin matafiya, hakan ba karamar asara zai janyo wa kasar ba.
” Muna kokarin kiyaye ‘yan najeriya ne daga cutar covid 19, shiyasa zamu kara jinkirtawa kadan. Amma akwai sabon jirgi mai gudu sosoai da muka siyo mai anfani da diesel. Da zaran an kammala shirye shiryen fara aiki dashi, Shugaban kasa zai kaddamar dashi, daga nan za muga yadda zamu iya fara jigalar matafiyan mu tare da lura da ka’idojin da hukumar lafiya ta gindaya ” inji Amaechi
A wani labarin mai kama da wannnan, wasu kungiyoyi sun bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sa a gudanar da bincike kan ministan sufuri, kan badakalar kwangilar dala miliyan ($195m) da sukayi zargin anyi wakaci wa tashi dasu.