CORONA: An Kulle Jihar Ekiti

Gwamnatin jihar Ekiti ta saka dokar hana fita a fadin jihar Ekiti inda dokar za ta fara aiki daga yau Litinin, 11 ga watan Janairun 2021.

Dokar za ta rinƙa aiki ne daga 8:00 na dare zuwa 6:00 na safe.

Gwamnatin jihar dai ta saka wannan doka ne a yunƙurinta na daƙile yaɗuwar annobar korona. Hakan ya sa gwamnatin ta kuma hana taruwar mutum sama da 20 a wuri guda har sai abin da hali ya yi.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Akinbowale Omole ya bayyana cewa gwamnati na son ɗaukar matakan daƙile cutar domin kare mutanen jihar.

Saka wannan doka na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar da ke daƙile cutuka masu yaɗuwa NCDC ta sanar da cewa waɗanda suka kamu da korona a Najeriya sun zarce 100,000.

Labarai Makamanta