CORONA: Ɗalibai 180 Sun Harbu Bayan Komawa Makaranta A Legas

Wani rahoton da jaridar The Nation ta wallafa ya nuna cewa dalibai da malaman wata makaranta mai zaman kanta dake unguwar Lekki, a jihar Legas sun kamu da mugunyar cutar nan ta CORONA.

Kwamishanan lafiyan Jihar Legas, Mista Akin Abayomi, ya ce an gano sun kamu da cutar ne bayan binciken da aka gudanar a makarantar.

Kwamishanan yayin da yake bayanin binciken, ya ce wata daliba mai shekara 14, yar ajin SS1 ta fara rashin lafiya ranar 3 ga Oktoba kuma aka tura ta gida bayan karamin jinyar da tayi a makarantan.Kwana uku bayan hakan wani dalibi ya kamu da cutar bayan gwajin da akayi masa ranar 6 ga Oktoba.

Abayomi ya tabbatarwa jama’ar jihar Legas cewa gwamnati na daukan matakan da ya kamata domin shawo kan lamarin. Ya bayyana cewa an sanar da dukkan iyaye kuma an shawarcesu kan abinda ake ciki a ranar 13 ga Oktoba.

Labarai Makamanta