Ciyar Da ‘Yan Makaranta: Mun Kashe Naira Miliyan 500 Lokacin Kulle – Ministar Jin Ƙai

Ministar jin kai da kula da ibtila’i, Sadiya Umar Farouk ta bayyana cewa naira milyan 523.3 gwamnati ta kashe wajen ciyar da yara ‘yan makaranta a gidajen su.

Ta bayyana hakan ne a lokacin ganawar manema labarai da kwamitin yaki da cutar Corona virus a jiya Litinin.

Ta ce tsarin ba wai na ma’aikatar ta bane kamar yadda wasu ke tunani.

Tace kwamitin dake yaki da cutar Corona virus ne ya bada shawarar yin haka aka kuma tattauna har da gwamnoni aka yadda cewa gwamnatin tarayya ta bayar da kudi su kuma jihohin su kula da rabon kayan.

Tace an yi rabonne a Abuja, Ogun da Legas kawai. Tace ta kuma gayyaci hukumomin EFCC, ICPC, da DSS da dai sauransu ciki hadda kungiyoyin agaji suka saka ido kan aikin.

Tace suna ciyar da kowane yaro akan Naira 70 ne a rana, cikin abincin makaranta da ake ba yaran. Tace to sun yi kiyasin cewa kowane gida na da yara 3 dan haka suka rika bada kayan abincin daidai dana kwanaki 20 dake cikin wata na zuwa makaranta.

Labarai Makamanta

Leave a Reply