Ciwon ‘Ya Mace: Sun Sayi Mota Domin Kai ‘Yan Uwansu Mata Asibiti

Matan wadanda suke zaune a wani kauye da ake kira Bordo a karamar hukumar Jahun da ke jihar Jigawa a Nijeriya sun yi karo-karon kudi inda suka sayo motar daukar mata masu juna biyu zuwa asibiti domin haihuwa.

Matan sun samar da kudin ne inda aka sayi motar domin a rinka kai matan kauyen asibiti idan bukatar hakan ta taso musammamma haihuwa saboda matsalar sufuri da ake fuskanta a yankin.

Daga kauyen zuwa asibitin Jahun da ake kai matan haihuwa akwai tazarar kilomita 29, kuma kauyen ya kasance a lungu yake ga rashin kyawun hanya saboda ramuka.

Malama Halima Adamu, ita ta jagoranci yadda aka hada kudin da suka sayi motar ta kuma shaida wa ma nema labarai cewa, da naira dubu ɗai-ɗai suka tara kudin sayen motar inda suka bukaci kowacce mace a kauyen da ta bayar da nata kudin.
Ta ce:

“Da dubu dai-dai duk wata muka rinka tara kudinmu har sai da muka tara naira miliyan guda, a haka muka bayar aka saya mana motar, yanzu ga shi komai dare idan mace ta tashi haihuwa za a dauko motar a kai ta asibiti ta haihu lafiya a kuma dawo da ita lafiya”.

“Idan irin wannan tafiya ta tashi ta zuwa asibiti a haihu, to maigidan mai haihuwar zai bayar da naira dubu biyu, a ciki za a sayi mai na Naira 1500, dari biyar kuma sai a bawa ma’aji ya hada a cikin sauran kudin da muka tara saboda koda wani gyara zai iya tasowa,” in ji ta.

Labarai Makamanta

Leave a Reply