Cire Tallafin Mai: Majalisa Ta Amince A Kashe Biliyan 500 Wajen Rage Radadi

Majalisar wakilai ta yi na’am da bukatar Shugaban kasa Bola Tinubu da ciyo bashin naira biliyan 500 Za a yi amfani da kudin ne wajen siyawa yan Najeriya kayan tallafi domin rage masu radadin cire tallafin man fetur Majalisar ta amince da bukatar ne a zamanta na ranar Alhamis, 13 ga watan Yuli.

Majalisar ta amince da hakan ne bayan bukatar da Tinubu ya gabatar na daukar naira biliyan 500 domin tallafawa yan Najeriya da nufin rage masu radadin janye tallafin man Fetur.

Bukatar ta tsallake karatu na farko, na biyu da na uku a yayin zaman majalisa a ranar Laraba, 12 ga watan Yuli. Sai dai kuma, majalisar ta amince da bukatar shugaban kasar a ranar Alhamis, 13 ga watan Yuli bayan mambobin majalisar sun bayar da gudunmawa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply