Cire Bashi Da Ruwa: Majalisar Musulunci Ta Yaba Babban Banki

Daga Adamu Shehu Bauchi

Majalisar koli ta Addinin Musulunci a Najeriya ta yaba da cire kudin ruwa na bashin babban bakin kasan, don habbaka tattalin arziki ta fanin noma da kananan manana’antu a dalilin annobar corona.

Hakan yana kunshe ne a wata hira da Parfesa Salihu Shehu mataimakin babban sakatare na majalisar kolin yayi da kafar watsa labarai ta BBC sashen hausa.

Tun a baya dai yan Najeriya musamman ma musulmai sun jima suna wasiwasin karbar bashi mai ruwa daga babban bankin na Najeriya, domin abinda ka iya biyo baya a addinanche, kan cin kudin ruwa wato (interest) a turance.

Parfesan, yace to yanzu da wan nan yunkuri na babban bakin, musulamai a ko’ina a fadin Najeriya zasu iya cin wan nan gajiya na bashin farfadu da tattalin arzikin da ya durkushe, a sakamakun cutar korona da ta addabi duniya bama Najeriya kadai ba.

Shehu yaci gaba da cewa “Duk wani tallafin da ake bayarwa mulusulmi dayawa basu nema saboda gudun mu’ammala da ruwa wan nan yasa musulman da yawa basu samun irin moriyar da ake samu daga dukiyar kasa, don haka sun zama cici baya kan tattalin arzikin kasa duwani abu da za a bayar na tallafi sai kaga akwai kudin ruwa, mutanenmu baza su iya ba sai kaga mutum ya gwammace ya zauna a cikin talaucinsa da yayi mu’amulla da kudin ruwa”

Babban mataimakin Sakataren, ya kara da cewa “alfanun da za a samu yana da yawa domin ya fadada yadda mutane zasu shiga irin wan nan tsare-tsare gabansu gadi, ba tare da wata fargaba ba kai tasye kowa zai nemi wan nan domin habba ka tattalin arzikinsa saboda haka masu kananan sana’oi harkar noma harkar ilimi samar da cibiyoyi, batu na lafiya kowa zai shiga don haka wata dama ce da zata taimaki al’ummar mu”.

Shehu ya karkare da kira ga musulmai dasu tashi kada ayi nawa domin cin gajiyar wan nan mataki, kungiyoyin addini musulmi da sarakuna na arewa da shuwagabbani, hakimai, dagatai, dasu tashi don wayar da kan mutane lallai aje a ci wan nan bashin kada ayi kasa a gwiwa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply