Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Cin Hanci Da Rashawa: Sunusi Ya Bada Magani

Tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya magantu kan musababbin da ya sanya mummunar dabi’a ta cin hanci da rashawa ta ke ci gaba da tsananta a Najeriya.

Sarki Sanusi ya ce dabi’a ta cin da rashawa za ta ci gaba da fadada a kasar nan matukar za a ci gaba da samun mutanen da ba su cancanta suna rike mukamai da akalar jagoranci a kasar.

Haka zalika tsohon Gwamnan Babban Bankin na Najeriya, ya ce nuna wariya da ake yi wajen nadin mukamai ko kuma cike gurabe a wuraren aiki ya yi mummunan tasiri na ƙaruwar rashawa a kasar.

Ya ce babu ta yadda za a yi a samu wani ci gaba ko kuma kasar nan ta bunkasa idan har ‘yan kasar basu tsaya sun bi tsari na gaskiya ba da kuma cancanta wajen zaben shugabanni.

Yana cewa, ko shakka babu kasar nan za ta ci gaba da durkushewa a yayin da al’ummar kasar ke bin son zuciyarsu wajen zaben shugabanni a madadin su duba cancanta.

Furucin Sanusi II ya zo ne a ranar Juma’a yayin halartar wani taro ta yanar gizo da shirya a kan maudu’in ci gaba da wanzuwa da dorewar kasa da kuma al’umma.

Ya ce tunda dai ƙa’idodi da manufofin Hukumar Da’ar Ma’aikata suna kunshe a cikin Kundin Tsarin Mulki, akwai bukatar a rika duba izuwa masu kaifin basiri daga ko ina suke a fadin kasar yayin nadin mukamai.

Ya ce, “A magana da ta fuskar addini da kyakkyawar dabi’a, rashawa babbar matsala ce. Amma idan muka dube shi ta fuskar tattalin arziki, zamu fahimci cewa, ba rashawa bace kawai amma irin nau’in rashawar.”

“Wani bangare na matsalar da muke fama da ita shi ne rashin dacewa kuma shi ya sa na ci gaba da cewa dole ne mu mai da hankali kan duba zuwa ga cancanta.”

“Muna da tsari ake kira Da’ar Ma’aikata kuma na yi imanin cewa ya kamata mu samu ‘yan Najeriya daga ko’ina suka fito a fadin kasar wajen danka musu akalar shugabancin al’umma.”

“Amma ‘yan Najeriyar da za a bai wa madafan ikon ya zamana sun kasance mutanen da suka cancanta.”

Kamar yadda jaridar the Punch ta ruwaito, Sarki Sanusi ya kuma wassafa wasu jerin ginshikai uku na sauyin fasali da muddin an kiyaye daga yanzu zuwa shekaru 7 ko 10, za a samu kyakkyawan sauyi a kasar.

Daga ciki sun hadar da bukatar tabbatar da kudirin sauya dokar zabe da siyasa musamman yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima da kuma tattalin kudi gami da riko da cancanta a duk abinda aka sanya gaba.

Exit mobile version