Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi kira na gargadi ga shugabannin kasashen Afrika da su tashi tsaye wurjanjan domin tsamo nahiyar nan daga kangin rashawa.
Wannan gargadi yana kunshe cikin wata sanarwa da Femi Adesina, hadimi na musamman kan sadarwa da hulda da al’umma ga shugaban kasar ya fitar a ranar Asabar.
Adesina ya sanar da cewa, Buhari ya yi wannan kira ne cikin wata wasika da ya aikewa da shugaban kasar Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa.
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, Ramaphosa shi ne shugaban kungiyar kasashen nahiyar Afrika yayin tunawa da ranar yaki da cin hanci da rashawa.
A wani rahoto da wakilinmu ya ruwaito, shugaba Muhammadu Buhari ya yi magana a kan binciken da ake yi wa dakataccen mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin zagon kasa (EFCC).
A wata takarda da Garba Shehu, babban mataimaki na musamman a fannin yada labarai ga shugaban kasar, ya yi bayanin dalilin da yasa ya aminta da dakatar da Magu.
“An samu korafi daban-daban a kan mukaddashin shugaban hukumar EFCC. Bayan bincike na farko, an kira jami’an da ke karkashinsa inda aka bincikesu. “A saboda haka aka kafa kwamitin bincike mai kiyaye dokokin hukumar.
“A duk lokacin da ake zargin shugaban wata hukuma, a kan bukaceshi da ya dakata da aiiki don a samu damar yin bincike ba tare da wata matsala ba. “EFCC bata dogaro da yanayin mutum, a don haka bata sassauta wa kowa.
“EFCC na da zakakurai, jajirtattun ma’aikata maza da mata masu fatan kiyaye dukkan dokokin kasar nan tare da mika duk wanda ya zo da almundahana gaban hukuma.
“Amma kuma, an bai wa Magu damar da zai kare kansa tare da amsa tambayoyin da ake masa. Hakan ce kuwa ta kamata a karkashin dokar kasar nan wacce ta bai wa kowa damar kare kansa,” .
Garba Shehu ya kara da cewa, dole ne a gane cewa yaki da rashawa a kasar nan ba a wuri daya ake tsayawa ba. Ta kowanne fanni ana kokarin tabbatar da shi.