Cin Hanci Da Rashawa: Hukumar Shige Da Fice Ta Kori Jami’ai 60

Hukumar Kula da Shiga da Fice ta Ƙasa ta ce ta kori jami’anta 60 bayan an kama su suna karɓa ko bada toshiyar baki.

Shugaban hukumar, Muhammad Babandede ne ya sanar da hakan a hirar sa da BBC Hausa a ranar Asabar 10 ga watan Oktoba.

Ya kuma ce ya taɓa yin ɓadda-kama a matsayin mai shara domin ya cafke masu karɓar toshiyar baki.

Babandede ya ce an kori jami’an 60 ne cikin shekaru hudu da suka shude bayan anyi ƙarar su “tare da hujjoji” da aka gabatar wa hukumar ta hannun Ma’aikatan Harkokin Cikin Gida.

“Kimanin shekaru hudu kenan da muka hana bada toshiyar baki don tura jami’ai wuraren ayyuka masu kyau kamar yadda aka saba a baya.

Ƙarƙashin Ma’aikatar Cikin Gida, Mun sallami jami’ai 60 da aka kama da laifin rashawa a filayen jiragen sama da toshoshin ruwa,” in ji shi.

“Akwai gurɓatattun jami’ai har cikin manya. Amma hakkin mu ne a matsayin shugabanni mu hana hakan musamman batun bada cin hanci don tura jami’ai boda da tashoshin jiragen ruwa.

Mun kuma hana jam’i a da ke aiki a wuraren kai wa manyan su kudi. Duk wanda aka kama zai gane kurensa.

Na taɓa yin shiga irin ta masu shara a filin tashin jiragen sama da tashan jirgin ruwa don in kama gurɓatattun jami’ai. Ba zamu iya aikin mu kadai ba musamman yanzu da sauran hukumomin tsaro ke taya mu tsare iyakokin ƙasa,” in ji Babandede.

Har wa yau, ya ce dole duk wata hujja da za a gabatar game da jam’in da ake zargi da karɓa ko bada rashawa ya zama sahihi.

Labarai Makamanta

Leave a Reply