An bayyana matakin da Kotun kolin tarayya ta dauka na ba wa ƙananan hukumomi ‘yancin gashin kansu da hana gwamnoni yi musu katsalandan, da cewar mataki ne na nasara kuma abin a yaba.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin wani jigo a jam’iyyar PDP na Jihar kaduna, kuma ɗan takarar Shugabancin jam’iyyar a jihar Mr Edward Auta, a yayin wata ganawa da suka yi da wakilinmu a Kaduna.
Ɗan Siyasar ya kara da cewar sai dai wani hanzari ba gudu ba, ya kamata a faɗaɗa al’amarin ya zuwa ga zaɓukan ƙananan hukumomi, ya zamana an cire zaɓukan daga gwamnatin jihohi zuwa hukumar zaɓe ta kasa INEC.
“Idan kayi la’akari za kaga cewa kasancewar harkar gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomi na hannun jihohi shi ya sa a duk lokacin da aka gudanar da zaɓe sai ace jam’iyya mai mulki ita ce ta lashe dukkanin kujerun kananan hukumomin, kuma kowa ya sani ‘yan amshin shatan gwamna ne kawai ake zaba, saboda haka koda ya zamana an tsame gwamnonin daga harkar kuɗin ƙananan hukumomi amma duk da haka zai kasance yaran sune a shugabancin ƙananan hukumomin, kaga an gudu ba a tsira ba kenan, an baka kyauta da hannun dama an kwace da hannun hagu”