Hukumar kula da ayyukan yan sanda (PSC) ta sanar da sallamar wasu manyan jami’an rundunar ‘yan sanda guda hu?u bisa laifukan da suka shafi cin amana da nuna rashin kwarewa a aiki.
Hakan na kunshe ne a cikin wata takarda da shugaban hukumar, Ikechukwu Ani, ya fitar tare da aika sako zuwa ga manema labarai a ranar Lahadi, a Jihar Lagos.
Mr Ani ya ce, hukumar ta ?auki wannan matakin ne yayin wani zaman ganawa da hukumar ta yi ranar Juma’ar da ta gabata.
“An sallami babban Sufuritanda (CSP) na ‘yan sanda bisa rashin gaskiya da nuna halayen da suka yi hannun riga da na jami’in tsaron ?asa.
“Sannan an kara sallamar wani jami’in dan sanda mai mukamin Sufuritanda (SP) bayan samunsa da laifin ha?a baki tare da wasu batagari guda hudu domin sace na’urar rarraba hasken wutar lantarki a cikin unguwa; wato taransifoma.
Kazalika hukumar PCS ta bayar da umarnin a gurfanar da shi saboda rasin gaskiyar da ya nuna da kuma cin amanar aikin dan sanda.
“Sai kuma karin wasu manyan jami’an guda biyu da suka hada da babban mataimakan Sufuritanda (DSP) da mataimakin Sufuritanda (ASP), a cewar Ani.
Ani ya kara da cewa; “mataimakin Sufuritandan (ASP) ya jagoranci shigo da makamai ta barauniyar hanya daga kasar Benin. “Shi kuwa DSP an same shi da laifin fitar da wasikar bogi domin rakiyar wata kwambar motocin SARS da zummar an sake su ne a hukumance.
Sa’ar da aka yi lokacin sojoji na kan aikin bincike kan hanyar da suka je wucewa, suka binciki kayan dake cikin motocin.
DSP din da abokan laifinsa sun tsere, sun bar motocin a nan.” Ani ya tabbatar da cewa kowanne cikin su zai fuskanci fushin hukuma.