Cin Amanar Ƙasa: Tilas Magu Ya Gurfana Gaban Ƙuliya

Jam’iyyar PDP bayan data nazarci dukkan zarge zargen da ake shugaban riko na hukumar dake kula da cin hanci da rashawa Ibrahim Magu, ya zama dole ya fuskanci shari’a.

Jam’iyyar tace wannan ya tabbatar da zargin da da zargin cin hamci da mukewa EFCC, a karkashin mulkinsa, cikakken dan cin hancine wanda ya sace dukiyar da aka dawo da ita , ya dunga kama yan adawa, ya dunga karbar kudade daga hannun yan Najeriya wanda basuji ba basu gani ba.

Jam’iyyar tace ta gamsu da dukkan zargin da ministan shari’a da kuma ma’aikatar tsaro ta farin kaya suke ma hukumar EFCC din ta mallakawa kansa inda Magu ya mallakawa kansa gidajen da aka kwato, wanda wannan ya nuna duk maganar da APC take na yaki da cin hanci da rashawa karyace.

Wannan ya kara nunawa duniya abun da yasa cin hanci yake karuwa a mulkin Buhari ba, wanda dama kungiyoyi da dama masu zaman kansu na duniya sun sha yin wannan zargin irinsu (TI).

Abun kunyane ga kasar nan, ace mutumin da yake jagorantar yaki da cin hanci da rashawa kuma karkashin jagorancin shugaban yaki da rashawa na afrika (AU) kuma wanda yake tutiya da tabbatar da kawo karshen cin hamci, amma an kama da wawashe dukiyar mutane da al’mundahana.

Wannan ya tabbatar da dukkan maganar da Buhari yake ta yaki da cin hanci da rashawa karyace domin gana karkashinsa nan irin shi shugaban EFCC din sun wawashe dukiyar mutane.

Abun da yan Najeriya suke zato a wajen shugaban kasa Buhari shine yabar doka tayi aikinta wajen ganin an tabbatar da an gurfanar da Magj a gaban kotu.

Duk wani abu sabanin haka yan Najeriya bazasu amince ba.

Sa hannu
Kola Ologbondiyan
Sakataren watsa labarai

Labarai Makamanta

Leave a Reply