Kwamitin fadar shugaban kasa da aka nada domin binciken dakataccen shugaban hukumar hana almundahana EFCC, Ibrahim Magu, ta bada shawara a sallami Magu.
A labarin da The Cable ta samu, kwamitin karkashin jagorancin tsohon Alkalin kotun daukaka kara, Ayo Isah Salami, ta baiwa Buhari jerin shawarin da tayi kuma daga ciki shine a hukunta Magu kan zargin rashawa da ci da kujerarsa.
An zargi Magu da saba dokar CCB ta hanyar kin bayyana wasu dukiyoyin da ya mallaka lokacin da ya shiga ofis a 2015.
Hakazalika, kwamitin ta baiwa Buhari shawaran cewa ya nada sabon shugaban EFCC ba tare da bata lokaci ba.
Hakan na bisa umurnin da shugaba Buhari ya yiwa mambobin kwamitin ranar 3 ga Yuli, 2020 cewa su “rika bashi rahoto lokaci bayan lokaci.”
Tsohon diraktan ayyuka a EFCC, Mohammed Umar, ke jan ragamar lamura a hukumar tun ranar 6 ga Yuli bayan dakatad da Magu.
An dakatad da Magu daga ofishinsa ne ranar 7 ga Yuli, 2020 bayan zarginsa da ake yi.
Magu ya shiga tsaka mai wuya ne bayan takardar tuhumar da ministan shari’a, Abubakar Malami, ya rubuta kansa na laifinsa rashawa.
Ga jerin tuhume-tuhume 10 cikin 22 da ake yiwa Ibrahim Magu
- Tufka da warwara wajen lissafin kudaden da EFCC ta kwato hannun barayin gwamnati
- Ikirarin cewa N539bn aka kwato maimakon N504bn
- Rashin biyayya ga ofishin Antoni Janar na tarayya
- Rashin gabatar da isassun hujjoji domin dawo da Diezani Alison-Madueke Najeriya
- Bata lokaci wajen binciken kamfanin P&ID wanda ahakan ya kai ga rikicin da ake a Kotu yanzu
- Kin bin umurnin kotu na sakin asusun wani tsohon diraktan banki kimanin N7bn
- Bata lokaci wajen daukan mataki kan jiragen ruwa biyu da hukumar Sojin ruwa ta kwace
- Fifita wasu jami’an EFCC kan wasu wadanda akafi sani da ‘Magu Boys’
- Kai wasu Alkalai kara wajen shugabanninsu ba tare da sanar da Antoni Janar ba
- Sayar da dukiyoyin sata ga yan’wansa, abokan arziki da abokan aiki