Darakta Janar ta Hukumar Kula da Abinci ta Kasa, NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta shawarci ‘yan Najeriya da su kaurace wa ajiye dafaffen abinci a cikin firiji sama da kwanaki uku.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai ba da shawara kan harkokin yada labarai na hukumar, Sayo Akintola, ya sanya wa hannu a ranar Talata.
Hukumar ta yi gargadin cewa dafaffen abincin da aka ajiye a cikin firij na kwanaki zai fuskanci gurbacewar cututtuka da za su iya kaiwa ga mutuwa.
Wasu sassan sanarwar sun bayyana cewa: “Ta (NAFDAC FG) ta bukaci ‘yan Najeriya da su guji ajiye dafaffen abinci a cikin firij har na tsawon kwanaki uku, tana mai gargadin cewa dafaffen abincin da ake ajiyewa a cikin firij na kwanaki yana da saukin kamuwa da cututtuka masu haddasa cututtuka, mahimmi. masu cutar da abinci da ke haifar da mutuwa.”