Chadi: ?an Marigayi Idriss Deby Ya Zama Sabon Shugaban Kasa

An na?a Mahamat Idriss Deby Itno a matsayin shugaban gwamnatin ri?o a kasar Chadi.

Matakin ya biyo bayan mutuwar mahaifinsa, Idriss Deby a yau Talata sakamakon raunukan da ya ji a kusa da kan iyakar Chadi da Libya inda ‘yan tawaye ke bore.

Shugaban na riko na da shekaru 37 a duniya kuma Mahamat Idriss Deby Itno babban janar na soja ne mai anini uku a rundunar sojin Chadi.

A wata sanarwa da ya gabatar a gidan talabijin, mai magana da yawun rundunar sojin ?asar Janar Azem Bermandoa Agouna ya ce, Shugaba Idriss Déby na Chadi “ya ja numfashinsa na ?arshe a yayin da yake kare martabar ?asar a fagen daga”.

Janar Mahamat Idriss Deby Itno

Majalisar ?oli ta soji za ta jagoranci ?asar har na tsawon wata 18 karkashin jagorancin Mahamat Idriss Deby

Mista Déby ya ?are mulkin ?asar ne tun a shekarar 1990.

A ?arshen mako ne ya je fagen daga don kai wa dakarun da ke ya?i da ?an tawaye ziyara a kusa da kan iyakar Libiya.

Deby ya rasu ne yayin da yake kan hanyar lashe za?e wa’adi na shida sakamakon za?en da aka gudanar ranar 11 ga watan Afrilu.

Related posts

Leave a Comment