Zaɓen Edo: Talakawa Sun Kunyata Masu Maguɗin Zaɓe – Kwankwaso

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya taya gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki murnar lashe zabe karo na biyu da yayi a karshen makon daya gabata. Kwankwaso ya wallafar hakan ne a shafinsa na Twitter. Kwankwaso yace , “Mutanen kirkin jihar Edo sunyi magana. Mutane sun nuna zabinsu na gaskiya. Don haka, inaso inyi amfani da wannan damar domin taya mutanen jihar Edo murnar gama zaben gwamnoni lafiya, kuma cikin kwanciyar hankali.” Ya kara da cewa, “Inaso in taya mutanen jihar Edo murna musamman saboda tsayuwa da dagewa wurin kara zabar jagora…

Cigaba Da Karantawa

Buhari Adalin Shugaba Ne Wanda Ba Ya Ƙarfa-Ƙarfa – El Rufa’i

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El Rufa’i ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari adali ne wanda bai taba yin amfani da kujerar shi ko isarsa ta hanyar da bata dace ba. El-Rufai ya sanar da hakan a ranar Litinin yayin tsokaci a kan zaben gwamnan jihar Edo da aka yi a ranar Asabar da ta gabata, wanda PDP ta yi nasara akan APC. A yayin jawabinsa a shirin Sunrise Daily, wani shiri na gidan talabijin na Channels, El-Rufai ya ce ya yi fatan APC za ta ci zaben. Kamar…

Cigaba Da Karantawa

Zaɓen Edo: Ba Mu Yarda Da Magudin Da INEC Ke Yi Ba – Oshiomole

Bayan bayyana nasarar jam’iyyar PDP a kananan hukomin takwas cikin goma sha biyu da INEC ta yi, tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomole ya ce ba za su amince da magudin da hukumar zabe take shirin shirya musu ba, domin babu adalci a ciki. A wani lamarin daban kuwa kwamishinan zaben ya sanar da harbe wani jami’in INEC a karamar hukumae Etsako, sannan kuma wani jami’in tattara sakamakon zabe shi ma ya yi batan dabo a wata karamar hukuma. Yayin da ya rage zaura sakamakon kananan hukumomi biyu…

Cigaba Da Karantawa

Zaɓen Edo: PDP Ta Yi Wa APC Fintinkau

Jam’iyyar PDP ta sha gaban jam’iyyar APC a yayin da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ke cigaba da sakin sakamakon zaben kujerar gwamnan jihar Edo. Hakan na nufin cewa dan takarar jam’iyyar PDP kuma gwamnan jihar Edo mai ci, Godwin Obaseki, ya na kan gaba da rinjaye mai yawa a yayin da ake cigaba da sakin sakamakon zaben. Ga wasu daga cikin sakamakon zaben kamar yadda INEC ta saki; Karamar hukumar Igueben PDP: 7,870 APC: 5,199 Karamar hukumar Esan central PDP: 10,964 APC: 6,719 Karamar hukumar Esan…

Cigaba Da Karantawa

Bauchi: APC Ta Yi Babban Kamu

Tsohon Sanata dake wakiltar Bauchi ta tsaskiya Isah Hamma Misau a Jihar Bauchi, yayi ban kwana da Jam’iyyar PDP inda ya hada kai da Dogara a Jam’iyyar APC. Tuni dai ruwa yayi tsami tsakanin Hamma Misau da Jamiyyar sa ta PDP da kuma gwamna Bala Mohammed dake jagoranci Jihar a halin yanzu, indai ba amanta ba Misau ya kasance a cikin yayan jam’iyyar da sukayi ruwa sukayi tsaki don ganin sun kada Jamiyyar APC a zaben gamagari na 2015. Kuma Jam’iyyar PDP har tabashi mukamin shugabanci kwamitin bankado al’mundahana da…

Cigaba Da Karantawa

Rashin Tausayi Ne Ƙarin Farashin Mai Da Lantarki A Yanzu – Ladaja

Hamshakin ‘dan kasuwan nan kuma tsohon ‘dan takarar shugabancin kasar nan a zaben 2019 da ya gabata, hon Ibrahim Abubakar Ladaja ya bayyana rashin jin dadin sa dangane da karin kudin wutar lantarki da man fetur da gwamnatin tarayya tayi. Hon Ibrahim ya bayyana cewa ” a irin halin da talakawan kasar nan ke ciki, bai kamata a kara masu kudin wuta ba. Kowa ya san halin da tattalin arzikin duniya ya shiga sakamakon bullar annobar cutar covid 19 daya tsayar da komai wuri daya. Kasar mu ta shiga halin…

Cigaba Da Karantawa

Zaɓen Edo: Ina Wasiyya Da Yin Zaɓe Cikin Lumana – Buhari

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya shawarci jam’iyyun siyasa da ‘yan takara da jami’an tsaro da su yi aiki tsakanin su da Allah a zaɓen gwamna da za a yi a Jihar Edo a ranar Asabar ɗin nan. A cikin saƙon da ya aike wa da masu zaɓe da jam’iyyun siyasa da jami’an zaɓe da na tsaro, shugaban ya kuma yi gargaɗi kan abin da ya kira “tunanin siyasa irin na ko-a-mutu-ko-ai-rai.” Mai taimaka wa shugaban ƙasa kan al’amurran aikin jarida da yaɗa labarai, Malam Garba Shehu, shi ne ya bada…

Cigaba Da Karantawa

Zaɓen Edo: ‘Yan Takara Sun Ƙulla Yarjejeniya

‘Yan takarar kujerar gwamna daga jam’iyyun siyasa daban-daban a jihar Edo da ke kudancin Nijeriya suka cimma yarjejeniyar zaman lafiya. Kwamitin zaman lafiya na kasa, karkashin tsohon shugaban Nijeriya, Abdussalami Abubakar ne ya shirya zaman yarjejeniyar. Ana dai zaman dar-dar game da zaben gwamnan da za a yi a jihar, ranar asabar mai zuwa, sakamakon rashin jituwar da ake samu tsakanin magoya bayan manyan jam’iyyun siyasar jihar, wato APC da PDP.

Cigaba Da Karantawa

Duk Wanda Ya Ce Akwai Yunwa A Najeriya Maƙaryaci Ne – Adamu Aliyu

Ɗaya daga cikin manyan na kusa da shugaba Muhammadu Buhari kuma tsohon dan majalisar wakilai, Farouq Adamu Aliyu, ya bayyana cewa duk masu cewa akwai yunwa a Najeriya makaryata ne. Adamu Aliyu ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin hira da yake a shirin gari ya waye (Sunrise) na tashar Channels. Dan siyasan yace a jiharsa ta Jigawa, babu yunwa kuma hakazalika sauran jihohin Najeriya. Yayinda aka yi masa tambaya da rahoton dake nuna cewa Najeriya ce cibiyar yunwa a duniya, Adamu Aliyu yace: “Ban tunanin gaskiya ne saboda jihata…

Cigaba Da Karantawa

Sukar Tinubu Ga Ɗan Takarar Mu Abin Dariya Ne – PDP

Jam’iyyar PDP tayi dariya da taga wani faifan bidiyan da jagoran APC ,Asiwaju Bola Tinubu ,inda yake kokarin hana dumukuradiyya tayi aikin ta inda yake nunawa mutane kamar bayinsa ne ,ko Allansu , inda yake kokarin zabawa mutanan Edo mutumin da zai jagorancesu . Muna mamakin yadda Asiwaju yake nunawa yan Najeriya isa da iko kamar shine ya kawo dumukuradiyya kasar nan,wanda kuma ba haka bane,inda mafi lokaci ma yake tozarta dumukuradiyya ta hanyar kin barin mutane su zabi abun da suke kauna, ya musu karya,yake yaudararsu ta hanyar nuna…

Cigaba Da Karantawa

Sukar Tinubu Ga Ɗan Takarar Mu Abin Dariya Ne – PDP

Jam’iyyar PDP tayi dariya da taga wani faifan bidiyan da jagoran APC ,Asiwaju Bola Tinubu ,inda yake kokarin hana dumukuradiyya tayi aikin ta inda yake nunawa mutane kamar bayinsa ne ,ko Allansu , inda yake kokarin zabawa mutanan Edo mutumin da zai jagorancesu . Muna mamakin yadda Asiwaju yake nunawa yan Najeriya isa da iko kamar shine ya kawo dumukuradiyya kasar nan,wanda kuma ba haka bane,inda mafi lokaci ma yake tozarta dumukuradiyya ta hanyar kin barin mutane su zabi abun da suke kauna, ya musu karya,yake yaudararsu ta hanyar nuna…

Cigaba Da Karantawa

Sukar Tinubu Ga Ɗan Takarar Mu Abin Dariya Ne -PDP

Jam’iyyar PDP tayi dariya da taga wani faifan bidiyan da jagoran APC ,Asiwaju Bola Tinubu ,inda yake kokarin hana dumukuradiyya tayi aikin ta inda yake nunawa mutane kamar bayinsa ne ,ko Ubangiji, inda yake kokarin zabawa mutanan Edo mutumin da zai jagorancesu . Muna mamakin yadda Asiwaju yake nunawa yan Najeriya isa da iko kamar shine ya kawo dumukuradiyya kasar nan,wanda kuma ba haka bane,inda mafi lokaci ma yake tozarta dumukuradiyya ta hanyar kin barin mutane su zabi abun da suke kauna, ya musu karya,yake yaudararsu ta hanyar nuna musu…

Cigaba Da Karantawa

Zaɓen Edo: Kar Ku Zaɓi Obaseki – Gargaɗin Tinubu

Babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu, ya yi kira ga al’ummar jihar Edo suyi watsi da gwamna Godwin Obaseki, dake neman zarcewa kan kujerarsa. A faifan bidiyon da tasahar TVC ta saki, Tinubu ya ce Obaseki ba jarumin demokradiyya bane kuma a yi waje da shi a zaben gwamnan ranar Asabar. Tinubu na cikin jiga-jigan APC da suka yiwa Obaseki yakin neman zabe a shekarar 2016 karkashin jam’iyyar APC.Amma daga baya, gwamna Obaseki ya fita daga APC zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) bayan rikicin da…

Cigaba Da Karantawa

Ku Yi Koyi Da Amurka Na Hana Masu Magudi Shiga Kasashen Ku – Saraki Ga Tarayyar Turai

Bukola Saraki, tsohon shugaban majalisar dattijai, ya nemi kasar Burtaniya da Tarayyar Turai da su bi kasar Amurka wajan hana masu magudin zabe a Najeriya shiga kasar su. Saraki ya yi wannan kiran ne a ranar Talata yayin da yake jawabi a wani taron da Cibiyar Raya ‘Yancin Dan Adam ta shirya domin bikin ranar Dimokuradiyya ta Duniya ta bana. A ranar Litinin, Amurka ta sanya takunkumin biza ga mutanen da suka dagula zaben gwamnoni a jihohin Kogi da Bayelsa, kimanin shekara guda bayan ta dauki irin wannan matakin a…

Cigaba Da Karantawa

Bauchi: Rabon Tallafin Ambaliyar Ruwa Ya Bar Baya Da Ƙura

Gwamnatin Jihar Bauchi ta raba kayan tallafi na ambaliyar ruwa da cutar mashakon numfashi ga mutane dubu uku da dari biyar 3,500 a karamar hukumar Warji, inda matasan gari sukayi warwason kayayyakin tallafin Jim kadan ne da barin mataimakin gwamnan Sanata Baba Tela wanda shine ya wakilci gwamnan jihar a wajen rabon kayan, matasan sukayi kukan kura, na in bakayi bani waje, sukayi dai-dai da kayan abincin kafin Jami’an tsaro su farga matasan sunyi abinda suke so. In ba a manta ba, a kwanan baya ne ruwan sama yayi ambaliyar…

Cigaba Da Karantawa

Bauchi: Cin Hanci Da Rashawa Ya Mamaye Albashin Jihar – Bala

Gwamnan Jihar Bauchi Bala Abdulkadir Mohammed ya lashi takobin zakulu wadanda suke da hannu a cinhanci da rashawar da yayi katutu a biyan albashin ma aikata dana yan pansho, da kuma alawos-alawos a dukkannin fadin Jihar. Yayi wan nan furucin ne a wani taro na mussaman da yakira a makon jiya, tare da masu ruwa da tsaki kan wan nan badakala na albashin da yaki ci yaki cinyewa a fadin Jihar. Taron ya gudana ne a dakin taro na wajen saukan baki na rundunar sojin kasa dake Bauchi, (Command Guest…

Cigaba Da Karantawa

Zamfara: ‘Ya’yan APC Sun Yi Zanga-zangar Sakin Shugaban Su

Daruruwan ‘yan jam’iyyar APC a jihar Zamfara a ranar Lahadi sun tsinkayi hedkwatar ‘yan sandan jihar da ke Gusau, inda suka mika bukatarsu ta sakin shugabansu, Abu Dan-Tabawa da sauransu. An kama Dan-Tabawa sakamakon ganinsa da aka yi dumu-dumu yana taro da ‘yan bindigar daji, kamar yadda hadimin gwamnan jihar Zamfara, Zailani Baffa ya sanar. Masu zanga-zangar sun bayyana dauke da takardu kala-kala inda suke zargin kwamishinan ‘yan sandan jihar, Usman Nagogo da saka siyasa a lamarinsa ta yadda yake cafke ‘yan jam’iyyar daya bayan daya a jihar. A yammacin…

Cigaba Da Karantawa

2023: An Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu

Wata kungiyar siyasa mai suna BAT 23, ta kaddamar da yakin neman zabe da kuma tattara masoya ga shugaban jam’iyyar APC, Bola Tinubu a zaben shugabancin kasa da ke zuwa na 2023 a Abuja. An gano cewa Tinubu na kokarin fitowa takarar zaben shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC a kasar nan.Shugaban kungiyar, Umar Inusa, a yayin kaddamar da fara yakin neman zaben a Abuja a ranar sati, ya ce BAT 23 ta hada da dukkan magoya bayan Tinubu daga jihohi 36 na kasar nan tare da birnin tarayya, Abuja.…

Cigaba Da Karantawa

Za Mu Kawar Da Yunwa Nan Bada Jimawa Ba – Sadiya Da Nanono

Ma’aikatar Jin Kai ta Tarayyar Najeriya, da ci gaban Jama’a tare da ma’aikatar aikin gona sune zasu kafa tsarin ‘Zero Hunger Round Table’ da nufin kawar da yunwa nan da shekarar 2030 a duk fadin kasar nan. DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa Ma’aikatar ta fara taron Zero Hunger Roundtable ne a ranar 5 ga Mayu, 2020 tare da Shirin Abincin Duniya. Da take magana a taron Majalisar Tsaron Abinci na Kasa a ranar Alhamis a Fadar Shugaban Kasa, Minista Sadiya Umar-Farouk ta bayyana cewa an kirkiro da shirin ne a…

Cigaba Da Karantawa

Naira Biyar-Biyar Nake So Ku Turo Domin Na Waƙe Atiku – Zango

Shahararren jarumin finafinan Hausa, Adam A. Zango ya bayyana zaben gwamnatin APC a matsayin zaben tumun dare, don haka a shirye suke da su sake marawa jam’iyyar PDP baya don ganin ta dawo mulki karkashin jagorancin Atiku Abubakar. Zango ya ce yanzu haka Atiku yana kasar Dubai tun bayan zaben 2019, don haka yana kira da masoyan Atikun da kowane ya turo masa da akalla naira dari biyar-biyar domin yi masa wakar dawowa gida domin tunkarar zaben 2023. A faifan bidiyon da Zango ya bayyana hakan, ya bada asusun ajiyar…

Cigaba Da Karantawa