Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahim Alhamis, ashirin da shida ga watan Rabi’ul Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammas S.A.W. Daidai da goma sha biyu ga watan Nuwamba na shekarar 2020. Ana cikin makokin rasuwar Dan Iyan Zazzau Hakimin Kabala Alhaji Yusuf Ladan, sai kuma ga rasuwar tsohon gwamnan tsohuwar jihar Kaduna Alhaji Abdullkadir Balarabe Musa. Kamar ‘yan soshiyal midiya sun san ya kusan rasuwa, suka dinga sa dinbin ayyukan da ya yi cikin dan lokacin da ya yi yana gwamnan jihar Kaduna daga watan…

Cigaba Da Karantawa

Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Laraba ta Bawa ranar samu, ashirin da biyar ga watan Rabi’ul Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin Annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha daya ga watan Nuwamba, na shekarar 2020. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani tsari na tallafa wa matasa manoma. Mataimakiyar Shugaban Majalisae Dinkin Duniya Amina Mohammad, ta gana da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, da alkawarin Majalisar za ta tallafa wa wasu kasashe har da Nijeriya, su samu su farfado daga halin da suka shiga na…

Cigaba Da Karantawa

Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Talata, ashirin da hudu ga watan Rabi’ul Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin Annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma ga watan Nuwamba, na shekarar 2020. Yau goma ga watan Nuwamba, wato arba’in da daya ga watan Oktoba ga yawancin ma’aikatan Gwamnatin Tarayya bangaren ilimi. Bari in muku gwari-gwari. Har yau yawancin ma’aikata, misali na kwalejin foliteknik ta Kaduna ba su ga albashin watan jiya ba. Kuma sun kusan shekara ko ma fiye da shiga tsarin IPPIS. Haka ma albashin watan Satumba,…

Cigaba Da Karantawa

Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Litinin, ashirin da uku ga watan Rabi’ul Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin Annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da tara ga watan Nuwamba, na shekarar 2020. Ina ta lekawa Cibiyar Da Ke Aikin Dakile Cututtuka ta Kasa NCDC a takaice har zuwa asubahin nan ban ga ta fitar da sabbin alkaluman wadanda suka harbu da cutar kwaronabairos ba. Ko kudin da ke hannunsu ya kare ne sai an kuma hankada musu wasu? Mayakan Sama sun far ma wasu barayin shanu da ke…

Cigaba Da Karantawa

Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Lahadi, ashirin da biyu ga watan Rabi’ul Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da takwas ga watan Nuwamba, shekarar 2020. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya taya Joe Biden murnar nasarar lashe zaben shugaban kasa Amurka da ya yi. Da kira ga Biden ya lalubo hanyoyin hadin kai tsakanin Nijeriya da Amurka, da kuma tallafa wa kasashen Afirka. Ta dai tabbata Joe ya tika Trump da kasa. Joe na da kuri’a 273, Trump yana da 213. Joe zai…

Cigaba Da Karantawa

Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Lahadi, ashirin da biyu ga watan Rabi’ul Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da takwas ga watan Nuwamba, shekarar 2020. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya taya Joe Biden murnar nasarar lashe zaben shugaban kasa Amurka da ya yi. Da kira ga Biden ya lalubo hanyoyin hadin kai tsakanin Nijeriya da Amurka, da kuma tallafa wa kasashen Afirka. Ta dai tabbata Joe ya tika Trump da kasa. Joe na da kuri’a 273, Trump yana da 213. Joe zai…

Cigaba Da Karantawa

Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Juma’atu babbar rana, ashirin ga watan Rabi’ul Awwal, shekara ta 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitra, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da shida ga watan Nuwamba na shekarar 2020. Da alama mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru suna ta musu alkawarin hanya shiru. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe.…

Cigaba Da Karantawa

Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Alhamis, goma sha tara ga watan Rabi’ul Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da biyar ga watan Nuwamba, shekarar 2020. Jiya Ministoci suka soma yi wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bayani a kan aikin da ya tura kowannensu wajen mutanensa su tattaro, barnar da ta auku sakamakon zanga-zangar #ENDSARS. Fashola ya masa bayanin Legas. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 155 a jihohi da alkaluma kamar haka: Legas 85Abuja 23Ondo 18Ogun 8Kaduna 5Oyo 5Taraba 5Kano 3Ribas 2Binuwai 1…

Cigaba Da Karantawa

Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Laraba, goma sha takwas ga waran Rabi’ul Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da hudu ga watan Nuwamba, na shekarar 2020. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 137 a jihohi da alkaluma kamar haka: Legas 60Abiya 21Abuja 18Ribas 13Kaduna 5Oyo 4Edo 3Delta 2Imo 2Kanno 2Ogun 2Bauci 1Gwambe 1Nasarawa 1Neja 1Oshun 1 Jimillar da suka harbu 63,173Jimillar da suka warke 59,634Jimillar da ke jinya 2,388Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1, 151 Jiya na ga Nuhu Yunusa Tankarau…

Cigaba Da Karantawa

Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Talata, goma sha bakwai ga watan Rabi’ul Awwal, shekarar1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da uku ga watan Nuwamba, shekarar 2020. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 72 a jihohi da alkaluma kamar haka: Legas 57Abuja 6Ogun 4Kaduna 3Neja 2Ondo 2Filato 2Katsina 1Oyo 1 Jimillar da suka harbu 63,036Jimillar da suka warke 59,328Jimillar da ke jinya 2,561Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,147 Da alamu mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, sun auka…

Cigaba Da Karantawa

Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Litinin, goma sha shida ga watan Rabi’ul Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da biyu ga watan Nuwamba, na shekarar 2020. Yau daukacin manyan makarantu na gaba da sakandare mallakar gwamnatin jihar Kaduna za su koma makaranta. Haka nan duk makarantu na firamare da na sakandare za su koma makaranta tara ga wannan watan. ‘Yan sanda sun kama wadanda ake zargi sun yi wasoson kayayyaki a jihar Kaduna su casa”in da uku, wata ruwayar kuma ta ce…

Cigaba Da Karantawa

Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Asabar, goma sha hudu ga watan Rabi’ul Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da talatin da daya ga watan Oktoba, shekarar 2020. Shugaban ‘Yan Sandan Nijeriya Mohammed Adamu, ya ce babu gaskiya a zargin da kungiyar kare hakkin bil’Adama ta Aminasti ta yi cewa jami’an tsaro sun yi amfani da karfin tuwo har da kisa ga masu zanga-zangar lumana ta #ENDSARS. Ya ce ‘yan sanda ne ma masu zanga-zangar suka kashe, suka ji wa da dama rauni,…

Cigaba Da Karantawa

Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalama alaikum barkanmu da asubahin Juma’tu babbar rana, goma sha uku ga watan Rabi’ul Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da talatin ga watan Oktoba, shekarar 2020. Da yake ana cikin shagulgulan Maulidi, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bai wa ‘yan Nijeriya shawarar su yi koyi da halayen Annabi Muhammad S.A.W. da ke cike da kauna, da yafiya, da fahimta. Ya yi wannan kira ne a sakonsa na Maulidi. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce gaskiya tattalin arzikin Nijeriya ba zai iya…

Cigaba Da Karantawa

Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin alhamis, goma sha biyu ga watan Rabi’ul Awwa, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da tara ga watan Oktoba, shekarar 2020. Yau take ranar Maulidi, ranar 12 ga watan Rabi’ul Awwal da aka haifi Annabi Muhammad S.A.W. Har Gwamnatin Tarayya ta ba da hutun yau, domin shagulgulan na Maulidi. Gwamnatin jihar Kaduna ta cire dokar hana walwala a dukkan kananan hukumomi 23 da ke jihar. Dokar hana walwalar za ta dinga soma aiki ne daga karfe…

Cigaba Da Karantawa

Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Laraba, goma sha daya ga watan Rabi’ul Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da 28 ga watan Oktoba, na shekarar 2020. Af! A rana mai kamar ta yau 28 ga watan Oktoba na shekarar 2016 wato shekara hudu daidai, da karfe 6 da minti goma na bayan asubah, na yi wannan rubutun kamar haka: ‘Assalamu Alaikum Jama’a barkanmu da asubahin juma’atu babbar rana, kuma suna na Is’haq Idris Guibi. Juma’a biyu ba mu yi addu’a ba saboda…

Cigaba Da Karantawa

Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Talata, goma ga watan Rabi’ul Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da bakwai ga watan Oktoba, shekarar 2020. Gwamnatin tarayya ta ce ba ta ce sai wani gwamna ya jira, ta ba shi izini kafin ya raba kayan tallafi na kwaronabairos ba. Ita kuma Zahra Buhari ta ce ta gode wa Allah da aka yi wallakiya aka gane ba mahaifinta ne matsalar kasar nan ba. Rijiya na bayarwa guga ke hanawa. Kodayake gwamnatin tarayya ta…

Cigaba Da Karantawa

Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Litinin, tara ga wtatan Rabi’ul Awwal, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da shida ga watan Oktoba na shekarar 2020. Gwamnatin Tarayya ta ce akwai wata naira biliyan ashirin da biyar da za ta bayar, ta matasa ce, don magance tashin hankali na matasan. Jama’a na ci gaba da wasoson kayan abinci duk inda suka samu labari an adana kayan abinci, kuma na baya-bayan nan ita ce Yola. Suka fasa sito uku da har ta kai…

Cigaba Da Karantawa

Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Lahadi takwas ga watan Rabi’ul Awwal, shekarar1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da biyar ga watan Oktoba na shekarar 2020. Yau ashirin da biyar ga wata ya kamata a soma jin dilin-dilin na watan nan daga yau. Shugaban ‘yan sandan Nijeriya Muhammad Adamu ya ce zanga-zangar da wawushe kayan mutane da na gwamnati, da lalata kayan mutane da na gwamnati, da far ma wasu mutane masu zaman kansu da jami’an gwamnati, da kashe jami’an tsaro da sauran…

Cigaba Da Karantawa

Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Asabar, bakwai ga watan Rabi’ul Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da hudu ga watan Oktoba na shekarar 2020. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gudanar da wani taro da tsofaffin shugabanin kasar nan, su Yakubu Gowon, da Obasanjo, da Shonekan, da Babangida, da Abdulsalam Abubakar, da Jonathan a kan halin tsaro da kasar ke ciki. Buharin ya bayyana cewa a zanga-zangar #ENDSARS an kashe farar hula 51, da ‘yan sanda goma sha daya, da sojoji…

Cigaba Da Karantawa

Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Guiɓi

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Juma’atu babbar rana, shida ga watan Rabi’ul Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da uku ga watan Oktoba, na shekarar 2020. Jiya da karfe bakwai na almuru shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wa al’umar kasar nan jawabi ta gidajen rediyo da talabijin da sauran kafofi na intanet, bayan shawarar da ake ta ba shi musamman Majalisar Dattawa ta ya daure ya yi wa al’umar kasar nan jawabi saboda halin da ake ciki.A jawabin na…

Cigaba Da Karantawa