Rahotanni daga birnin Kano na bayyana cewar Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce babban burinsa a rayuwa shi ne ya gaji magabatansa kuma yanzu hakan ya tabbata, sauran abin da ya saura shine fatan cikawa da imani da addu’ar shiga aljanna.
Mai Martaba Sarkin na Kano ya bayyana hakan ne a cikin wata hira ta musamman da ya yi da sashin Hausa na BBC, Sarkin ya ce baya ga murnar gadar mahaifinsa da yake yi yana kuma murnar zaɓarsa da Allah ya yi domin ɗora masa nauyin taimaka wa al’ummarsa.
Ya bayyana haka ne yayin da ake shirin bikin ba shi sandar girma, yana mai cewa a halin yanzu murna biyu yake yi.
Kazalika sarkin ya bayyana matakan da ya ɗauka wajen sasantawa da ‘yan uwansa waɗanda suka nemi sarautar tare.