Rahotannin dake shigo mana daga babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar APC ta ?asa, Gwamna Mala Buni na jihar Yobe, ya gana da Sakataren kwamitinsa, John Akpanudoedehe.
Rahotanni sun bayyana cewar Mai Mala Buni ya gana da Sakataren ne domin yin watsi da takardar dake yawo cewa mambobin kwamitin sun tsige shi daga kujerarsa ta Sakatare.
Jam’iyyar APC dai na cigaba da fuskantar rikicin cikin gida tun bayan tafiyar da shugaban ?asa Buhari ya yi waje duba lafiyar sa.