Shugaban ?asa Muhammadu zai ziyarci birnin Landan da ke kasar Birtaniya domin a duba lafiyarsa a ranar yau Talata.
A wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar ranar Litinin da maraice, ta ce shugaban kasar zai tafi birnin Landon din ne domin ya ga likitan shi kamar yadda ya saba.
Sanarwar, wadda mai magana da yawun shugaban kasar Femi Adesina, ya sanyawa hannu ta ce Shugaba Buhari zai dawo gida Najeriya a mako na biyu na watan Afrilu mai zuwa.
“Shugaban kasa zai soma ganawa da jami’an tsaro da safe, daga bisani zai yi tafiyar,” in ji Mr Adesina.
Shugaba Buhari ya sha tafiya Landan domin duba lafiyarsa tun lokacin da ya fara jagorantar kasar a shekarar 2015.
A 2017, Shugaban ya kwashe kwanaki 150 a ?asar ta Burtaniya a wata tafiyar duba lafiyar da ba a bayyana abin da ke damun shi ba.
Buhari ya kara komawa Burtaniya a watan Mayun 2018 domin ganin likitansa, inda ya yi kwana hudu kacal a kasar.
A watan Nuwambar 2020 ne, mai dakin shugaban kasar Aisha Buhari, ta ce akwai bukatar inganta bangaren lafiya a Najeriya domin a rage tafiye-tafiyen neman magani kasashen waje.