Buhari Zai Ziyarci Ƙasar Mali A Yau

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau Alhamis zai bar birnin tarayya Abuja zuwa Bamako a Jamhuriyar Mali don kai ziyarar aiki ta kwana daya kamar yadda fadar shugaban kasa ta bayyana.

Ziyarar da Buhari zai kai Mali za ta zama karo na farko da Shugaban Kasar zai fita daga kasar tun bayan bullar annobar coronavirus da ta karade duniya.

Sanarwar da mai taimakawa shugaban kasa na musamman a fanin watsa labarai, Femi Adesina ya fitar ta ce an shirya tafiyar ne bayan da wakilin ECOWAS na musamman a Mali, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ziyarci Buhari.

Sanarwar ta ce Buhari da wasu shugabannin ECOWAS karkashin jagorancin shugaban Jamhuriyar Nijar, Issoufou Mahamadou sun shirya yin taro a Mali domin cigaba da tattaunawa kan yadda za a wareware rikicin da ke adabar kasar.

Shugaba mai masaukin baki, Ibrahim Boubacar Keita da shugabannin kasashen Senagal, Machy Sall, Nana Akufo-Addo na Ghana da Alassane Ouattara na Cote d’Ivoire suma za su hallarci taron.

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ziyarci Buhari tare da Mr Jean-Claude Kassi Brou a ranar Talata ne don yi wa Shugaba Buhari bayanin abinda ke faruwa a Mali haka ya saka shugabannin na ECOWAS suka yanke shawarar yin taron.

“Za mu tambayi shugaban Nijar, wanda kuma shine shugaban ECOWAS ya yi mana bayani daga nan kuma za mu san matakin da zamu dauka, ” a cewar Shugaba Buhari.

Labarai Makamanta

Leave a Reply