Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar mai girma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai yi jawabin bankwana ga ?asa baki-?aya a matsayin shugaban ?asa a ranar yau Lahadi, 28 ga watan Mayu.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Malam Garba Shehu ya fitar, ta ce Buhari zai yi jawabin ne da misalin karfe 7 na safe.
Sanarwar ta kuma bu?aci dukkan gidajen talabijin da radio da kuma sauran kafofin ya?a labaru na zamani da su nuna jawabin ta hanyar ha?a tashoshinsu da gidan talabijin na ?asa NTA da kuma gidan rediyon tarayya FRCN.
A ranar Litinin 29 ga watan Mayu ne, shugaba Buhari zai mi?a mulki ga sabon za?a??en shugaban ?asa Bola Tinubu, a daidai lokacin da yake kammala wa’adin mulkinsa karo na biyu na shekara takwas.
‘Yan Najeriya na ci gaba da bayyana ra’ayoyi mabanbanta dangane da Shugabancin Buhari na shekaru takwas daga 2015 zuwa 2023, wasu na yabo wasu na sukar salon shugabancin shugaban.