Buhari Zai Tafi Amurka Halartar Taron Shugabannin Afirka A Yau

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban kasaMuhammadu Buhari a yau Lahadi zai tafi Amurka domin halartar taron shugabannin ƙasashen Afirka da Amurka za ta karbi bakunci.

A cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga shugaban kan kafofin yada labarai, Malam Garba Shehu ya fitar yau Asabar, ya ce taron wanda za a gudanar daga ranar 13 zuwa 15 ga watan Disamba da shugaba Biden zai jagoranta, na da zimmar ganin ta yi aiki da gwamnatocin Afirka da kuma al’ummomin su da ke zama a ƙasar domin ƙarfafa dangantaka tsakanin Amurka da ƙasashen Afirka.

Ya kara da cewa taron na kara neman karin hanyoyin da za a bi don inganta huldar tattalin arziki da samar da zaman lafiya da tsaro da kuma shugabanci na gari.

Gwamnonin jihohin Bauchi da Kwara da kuma wasu ministoci da manyan jami’an gwamnati ne za su yi wa shugaban rakiya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply