Buhari Zai Sayar Da Kadarorin Gwamnati Domin Cike Gibin Kasafin Kudin 2023

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar sakamakon girman giɓin da ake da shi a kasafin kuɗin shekarar 2023, gwamnatin tarayya ta tsara sayar da wasu daga cikin kamfanonin lantarki don cike giɓin.

Gwamnatin ta ɗauki matakin ne yayin da ya rage ƙasa da wata shida ta sauka daga mulki.

Za a sayar da kadarorin cikin wata ukun farko na 2023, amma za a buɗe shirin sayar da su a wannan watan na Disamba zuwa ƙarshen Maris.

A watan Oktoba da ya gabata Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin na 2023 da ya kai naira tiriliyan 20 (dala miliyan 45) – kasafi na ƙarshe kenan da gwamnatinsa za ta yi.

Najeriya kan aiwatar da kasafin ne da kuɗin da take samu daga kuɗaɗen man fetur, wanda farashinsa ya gamu da cikas tun daga shekarar 2020, da kuma satar man da tsageru ke yi a yankin Neja-Delta da ke kudancin ƙasar.
Majalisa Ta Ƙi Amincewa Da Kasafin Kuɗin Shekarar 2023

Idan ba a manta ba Majalisar Dattawa ta ƙi amince wa da kasafin kudin ƙasar na shekarar 2023 a ya yin zaman majalisar na ranar Alhamis.

Shugaban Majalisar dattawa Ahmad Lawan ya ce rashin amincewa da kasafin kuɗin ya biyo bayan kurakurane da kasafin kudin ke kunshe shi, daga ɓangaren gwamanti.

“Sakamakon wasu ƙalubale, ba za mu iya karbar rahotan kwamitin kula da kasafin kudin ƙasar ba saboda, ya zo majalisa da matsaloli.

Ahamd Lawan ya ce sai a jiya majalisar dattawan sun kuma karɓar ƙarin wasu buƙatu daga shugaban Najeriya, na kari a kasafin kudin na wasu ayyukan na musamman na naira tirilliyan 23.7.

Ya ce ranar Larabar 28 ga Disambar da muke ciki, yanzu suka tsayar domin amincewa da kasafin.

Labarai Makamanta

Leave a Reply