Buhari Zai Karbi Sakamakon Binciken Magu A Yau

A yau jumma’a ne 20 ga watan nuwanba ake sa ran kwamitin da ya binciki tsohon shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu zai mika ruhotansa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Tun a watan Yuli shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa kwamiti karkashin Ayo Salami domin ya binciki zargin da ke wuyan Mista Ibrahim Magu.

Rahotanni daga jaridar Vanguard sun bayyana cewa an ga ‘yan kwamitin Salami a fadar shugaban kasa dauke da tulin takardun binciken da su ka yi.

Tsohon Alkalin babban kotun daukaka karar ya fada wa ‘yan jarida cewa abin da su ke jira kawai shi ne shugaban kasa ya karbi rahoton aikinsu a yau.

Kawo yanzu ba a samu burbushin abin da rahoton binciken kwamitin shugaban kasar ya kunsa ba.

Related posts

Leave a Comment