Buhari Zai Kai Ziyara Zamfara Yau Alhamis

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyara Jihar Zamfara a ranar yau Alhamis.

Gwamna Bello Matawalle ne ya bayyana hakan a wani taron gaggawa da ya yi da dukkan masu mukaman na gwamnatin a cikin gidan gwamnatin a daren ranar Talata.

Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya ce Buhari zai ziyarci jiharsa a ranar yau Alhamis.

Gwamnan ya ce shugaban kasar zai kai ziyara jihar ne don yi wa mutanen karamar hukumar Anka da na Bukkuyum jaje akan hare-haren da aka kai musu inda mutane da dama suka rasa rayukansu.

Gwamnan ya bukaci kowa ya kiyaye dokoki Matawalle ya ce: “An shirya komai musamman don tarbar shugaban kasar yadda ya dace. “Ina so in sanar da mutanen Jihar Zamfara cewa shugaban kasar zai kawo ziyara ranar Alhamis musamman don yi wa mutanen Anka da Bukkuyum jaje akan hare-haren da aka kai musu.”

Gwamnan ya bukaci duk mazaunan Jihar su kasance masu bin dokoki yayin da shugaban kasar ya kai ziyara.

Labarai Makamanta

Leave a Reply