Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Buhari Zai Kaddamar Da Sabbin Samfurin Takardun Naira A Yau

Shugaban ƙasa Najeriya Muhammadu Buhari zai ƙaddamar da sabbin takardun kuɗin naira da aka sake wa fasali ranar yau Laraba.

Gwamnan babban bankin ƙasar CBN Godwin Emefiele ne ya bayyana haka ga manema labarai ranar Talata a wajen taron kwamitin tsare-tsaren kuɗi.

Mista Emefele ya ce babban bankin ƙasar ba zai sauya ranar ƙarshe da ya saka na mayar da tsoffin kuɗin zuwa bankunan ƙasar domin sauya su da sabbin takardun kuɗin ba.

Ya ƙara da cewa shugaban zai ƙaddamar da sabbin takardun kuɗin a lokacin taron majalisar zartarwa na ƙasa.

Tun da a ranar 26 ga watan Oktoba ne dai gwamnan babban bankin ƙasar ya sanar da cewa za a sauya fasalin wasu takardun kuɗin ƙasar, inda ya ce sabbin kuɗin za su fara yawo daga ranar 15 ga watan Disamba, inda za a ci gaba da kashe su tare da tsoffin kuɗin har zuwa ranar 31 ga watan Janairun 2023, lokacin da za a daina karbar tsoffin ƙudin.

Exit mobile version