Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai ƙaddamar da aikin tono man fetur a jihohin Bauchi da Gombe.
An dai gano tarin arzikin man fetur a jihohin biyu shekaru biyu da suka gabata
An ruwaito ƙaramin ministan man fetur Timipre Sylva, na cewa ”Za a gudanar da bikin fara tono man ranar Talata 22 ga watan Nuwamba Inda shugaba Buhari tare da wasu daga cikin ministocinsa za su halarta”
A shekarar 2016 ne kamfanin mai na ƙasar NNPC ya ƙaddamar da aikin binciko man fetur a arewacin ƙasar, abin da ya kai ga gano ɗimbim albarkatun man fetur ɗin a jihohin Bauchi da Gombe da Borno da kuma jihar Niger
A yayin da ƙasar ke dogara da man da ake tonowa daga yankin Niger Delta, Wannan shi ne karo na farko da za a fara tono man a yankin arewacin ƙasar, bayan da rikicin Boko Haram ya hana yunƙurin tono man a jihar Borno.
A wani labarin na daban bankin bada lamuni na Duniya IMF ya bukaci gwamnatin tarayya da ta kaddamar da bincike akan man fetur din da kamfanin NNPC ya ce ana sha a cikin kasar da kuma irin kudaden tallafin da ake zubawa da sunan talaka.
IMF ya kuma bukaci bincike akan kudaden da kamfanin ke zubawa a lalitar gwamnati sakamakon irin gibin da ya gani bayan ziyarar aikin da jami’ansa suka kammala a Najeriya.
Bankin ya ce abin takaici ne yadda kamfanin ke tafka asara sakamakon kashe makudan kudade da biyan dimbin basussuka, yayin da ake hasashen karuwar basussukan nan gaba kadan, abin da ke yi wa kasar illa wajen samun damar karkatar da kudaden da take samu wajen ayyuka na musamman a bangaren ilimi da kula da lafiyar jama’a.