Buhari Zai Gabatar Da Kasafin Kudi A Yau Juma’a


Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar a wannan Juma’ar ce shugaban ?asa Muhammadu Buhari zai gabatar da kudirin kasafin kudin kasar na ba?i, wanda aka kiyasta zai kai naira tiriliyan goma sha tara.

Kasafin ku?in dai yana da gi?in da sai gwamnati ta hada da rance za ta cike fiye da rabin kasafin kudin.

?an majalisun dokokin kasa wato da majalisar dattawa da ta wakilai za su yi zama ne na ha?in gwiwa don bai wa Shugaba Buharin damar gabatar musu da kudirin kasafin na ba?i, wanda shi ne kasafin ku?i na ?arshe da zai gabatar a matsayinsa na shugaban Najeriya.

An dai ?iyasta cewa a kasafin ku?in na fiye da tiriliyan 19, za a samu gi?i na fiye da naira tiriliyan goma sha biyu, wanda sai gwamnati ta hada rance da sayar da wa?ansu kadarorin kafin ta cike shi.Wasu labaran da za ku so karantawa

Kazalika akwai batun tallafin mai, wanda shi ma ?arin dawainiya ne ga kasafin haka kuma zai iya janyo zazzafar  muhawara, kasancewar wasu goyon bayan gwamnati ta ci gaba da ba da tallafin, yayin da wasu kuma ke ganin cewa ya kamata a dakatar, saboda a nasu ra’ayin masu hada-hadar man sun fi talaka cin gajiyar tallafin.

Sai dai ?an majalisar da dama na da ra’ayin cewa akwai bukatar a jira a ga gangariyar abin da kasafin kudin ya kunsa.

Honarabul  Jafar Sulaiman Ribadu, ?an majalisar wakilai ne daga jihar Adamawa wanda ke cewa zai so su karbi kudirin kasafin kudin badin da zuciya daya inda ya ce yana fata duk wani ?an Najeriya zai mori kasafin ku?in 2023.

Kasafin wannan shekara mai karewa ya kai naira tiriliyon goma sha bakwai da doriya wanda hakan ke nufin na badi ya ?ara shi da naira tiriliyan biyu da ?oriya.

Sai dai Sanata Adamu Muhammad Bulkachuwa ya tabbatar da cewa an samu cikas wurin aiwatar da kasafin ku?in bana a wasu ?angarorin saboda rashin samun isassun ku?in da za a aiwatar da shi.

Sai dai ya ce ana sa ran kafin ?arshen shekara za a samu shigowar wasu ku?in da za a ci gaba da ayyuka.

A Najeriyar dai za a iya cewa zumu?i da ?okin sauraron kasafin ku?in shekara-shekarar ya ragu a tsakanin al`ummar kasar da dama, sakamakon yanke ?aunar da wasu ke yi suna zargin cewa sau da yawa fa?a ne kawai ba cikawa!

Related posts

Leave a Comment