Buhari Zai Bar Kyakkyawan Tarihi Da Ba Za A Manta Ba – Hadimin Buhari

Tarihin Shugaba Buhari Zai Kasance Mai Kyau Fiye Da Yadda Masu Sukar Sa Ke Shirin Ya Zamoam’iyar APC ta dare kujerar mulki a shekarar 2015 inda ta doke Gwamnati mai ci, ta zo cikin tsammani sosai kan Shugaban Muhammadu Buhari.

Shekaru biyar kenan ake ciki, Gwamnatin ta yi aiki ka’in da na’in don ganin ta cika da yawa cikin tsammanin da ake mata, kuma har yanzu tana kai, Ttbbas akwai wasu Hukunce Hukunce masu Sauri da dole ne a dauka don Dai daita kasar akan Tafarki Cigaba mai Dorewa.

Don Dakatar da rashin Sarrafa Dukiyar Al’umma ta hanyar da ba dai dai ba, Kawo karshen cin hanci da Rashawa dake da alaka da Tallafi kan Albarkatun Man Fetur, Lantarki, Takin Zamani da dai Sauran su, Gwamnatin ta dauki mataki dake kawo tafiyar hawainiya akan gyaran fuska kan Dokoki, Janje dama bada ‘yan kasuwa damar sanya farashi da Kansu.

Cire Tallafin Mai a wannan bangare abune da aka jima ake hangen sa a Gwamnatoci da suka gabata a matsayin wani babban Mataki da samun Mafita akan hanyar da ake bida don Chigaban kasa. Wadan nan wasu sauyi ne da yazamo wajibi daya zo a makare tsari kan tsari, shiri kan wani Shiri sunzo kuma sun Shude amma an rasa kwarin gwaiwar Daukar wannan muhimmin Mataki.

Cikin ‘yan kwanaki da suka Shude, an samu dayin ikirari da kwarin gwaiwar Jagorantan dai daitatuwar Al’amura, a gurin wasu banagen yanar gizo da wani Bangarori na kungiyar Kwadago da ‘yan Adawa suna gani kamar matakine da shawari mara kyau a lokaci da bai Dace ba.

Babu wani bakon abu a kashin gaskiya cewar kasar a halin yanzu tana yaki da kalubale daban daban tare da Cutar Korona, Wanda ya hada da karancin kudin shiga, kusan Durkushewar kasuwan Mai, Ambaliyan ruwa, Barazanar ‘yan ta’adda da Barayin Daji to amma dukka wadan nan Kalubale, duk wata Gwamnati na Gari dole ta dau matakai don dai daita jin dadin Al’umma.

A matsayin Jagora, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dau wadan nan mawuyacin mataki, Sanannu da wadanda ba Sanannu ba, a matsayin Shugaba saboda ya nuna Kwarin gwaiwa kan daukan irin wannan mataki daya dace kasancewa hakan yazamo wajibi in akayi dubi da halin da aka tsinci kai ciki.

Tarihi zai yi Adalci wa Shugaba Buhari, saboda,
Za’a tuna dashi a matsayin Shugaban kasa wanda ya bada gudumowa gaya ga Tattalin Arziki gakuma cigaban kasa ta hanyar kawo karshen Shedancin cin hanci dake lullube a tallafin Mai.

A kowace Mulkin farar hula, Sakamako mafi muhimmanci shine amincewar Al’umma da nuna goyon bayan kowani ‘Yan Najeriya, Shugaba Buhari ya nuna kundujewa matuka na Daukan wannan Babban Shiri da aka jagoran ta, wannan ba wani abu bane yasa face don Babban cigaba ga Al’umma masu Daraja. A yayin gudanar da gyare gyaren, Shugaban kasa yana bukatar Goyon baya da fahimtar dukkan nin ‘yan kasa baki daya tare da Jam’iyun Adawa, Kungiyoyin Kwadago da Kungiyoyin Fararen hula.

A wadan nan lokacin kalu bale, Shugaban kasa yana nan yana cigaba da dabbaka Manufofin Kawo Cigaba, Ba siyasa ba kawai Tarihi zai tuna dashi a fannonin masu kyau, mai makon sukar na Manema labari ko na ‘Yan adawa.

Mal. Garba Shehu:
Babban Mai Tallafawa Shugaban kasa A Kafofin Watsa Labarai da Wayar da kan Jama’a.
06 ga watan Satumba, 2020.

Labarai Makamanta