Buhari Ya Ziyarci Daura Sau Biyu Cikin Wata Biyu

A ranar Juma’a, 29 ga watan Janairu, 2021, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci birnin Daura ta jihar Katsina mahaifarsa, inda ake sa ran zai shafe ‘yan kwanaki.

Rahotanni sun tabbatar da cewa jirgin mai girma Muhammadu Buhari ya sauka ne ta babban filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’Adua da ke jihar Katsina.

Gwamna Aminu Bello Masari da mataimakinsa, Munir Yakubu, shugaban majalisar dokokin Katsina, da Alkalin Alkalan jihar su ka tarbi shugaban kasar.

Mai magana da yawun Shugaban ?asa Malam Garba Shehu, ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar a shafinsa na Facebook da yammacin Juma’a.

Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar, ya jagoranci sauran hakimai da Sarakan Masarautar Daura su ka tarbi Shugaban ?asa Buhari.

“A zamansa da zai yi a Daura, ana sa ran zai yi wasu abubuwa, daga ciki har da yin rajistar zama ‘dan APC da aikin tabbatar da zama ‘dan jam’iyya.” Inji Shehu.

Jawabin ya ce: “Shugaban kasar ya na ganin muhimmancin wannan aiki ga damukaradiyyar kasar nan da yunkurin kawo shugabanci na gari wajen cigaban kasa.”

Shehu ya ce ana sa ran Muhammadu Buhari zai koma babban birnin tarayya a ranar Talata, 2 ga watan Fubrairu, 2021, domin cigaba da ayyukan da ke gabansa.

Related posts

Leave a Comment