?ungiyar Gwamnonin Najeriya ta bayyana cewar a magana ta gaskiya yabon gwani ya zama dole, kuma ya wajaba a yaba gami da Jinjinawa Shugaban kasa Buhari bisa jajircewarshi na ya?ar ta’addanci da ganin tsaro ya dawo a dukkanin fa?in ?asar gaba daya.
Shugaban kungiyar gwamnonin Nigeria kuma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi ya bayyana hakan lokacin da yake tsokaci game da yadda makomar tsaro yake a mulkin Buhari, inda ya ce ta’addanci ya yi sauki a Nijeriya tun lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi ragamar mulki a 2015 idan aka kwatanta da baya.
Shugaban kungiyar Gwamnonin ya ce kowa na rayuwa cikin tsoro duk da cewa jam’iyyar da ke mulki a kasar ta samu nasarori kan yaki da ta’addanci amma akwai bukatar ta kara jajircewa.
Fayemi ya yi magana ne a ranar Asabar yayin taron shekara-shekara da babban faston cocin Covenant Christian Centre, Poju Oyemade ya shirya a Legas.
Da farko Fayemi ya ce ba zai yi tsokaci ba kan yadda ya ke kallon kamun ludayin gwamnatin jam’iyyar APC a kasar ba amma daga baya ya yi tsokaci kamar haka:
“A 2015, mun yi alkawurra da yawa amma alkawarin da ya fi daukan hankalin mutane shine gaskiya da rikon amana.” “Wasu da dama ba za su yarda da ni ba amma a batun ta’addanci mun samu sauki idan aka kwatanta da 2015 a lokacin da muka karbi mulki.
“Ka tuna da bam da aka saka a gidan Majalisar Dinkin Duniya, coci-coci da aka kona a Abuja, ana tsoron zuwa Abuja a lokacin da Arewa maso Gabas amma an samu sauki a shekaru hudu na mulkin Buhari.”
Gwamnan ya ce ta’addancin ya sake dawowa saboda yaduwar makamai da matsalolin kan iyakokin Nijeriya da ma rasuwar Shugaban Chadi Idriss Deby. Inda ya kara da cewa gwamnatin Buhari da APC tana duk mai yiwuwa domin ganin ta kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Nijeriya.