Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Buhari Ya Yi Ganawar Sirri Da Gwamnonin APC

Fadar shugaban Najeriya ta yi ?arin haske game da ziyarar da wasu gwamnonin jam’iyyar APC suka kai wa Shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja.

Mai magana da yawun shugaba Buhari, Malam Garba Shehu ya ce gwamnonin sun kai ziyarar ce domin yabawa shugaban kan yadda ya sa baki a rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar, wanda suka ce matakin da ya ?auka ya janyo an fara samun maslaha kan matsalolin cikin gida na jam’iyyar ta APC.

Garba Shehu ya shaida wa BBC cewa a ziyarar gwamnonin, an tattauna batutuwan da suka shafi tsaro baya ga na rikicin jam’iyyar.

Tsaro:

Game da batun tsaro, Garba Shehu ya ce an samu ci gaba sosai a fannin tsaro saboda “duk wanda ya san inda aka fito zuwa yanzu, ya san an samu gagarumar nasara a kan matsalar rashin tsaro,”
“Shi yankin Kudancin Kaduna ai abin da ake ta jaddawa shi ne yau duk hukuma duk ?arfinta duk so da take ta kawo zaman lafiya, al’umma da suke zaune a wurin suma su zamana suna shirin zaman lafiya.” in ji sa.

A cewarsa, ba a Kudancin Kaduna ka?ai aka samu nasara ba, a Borno da Yobe ma “abubuwa sun yi sau?i sosai.”
Da yake magana kan matsalar tsaro a Katsina da Zamfara, Garba Shehu ya ce “muna tafe, nan ?in ma za a ga tatas an gama da shi” tun da a baya matsalar tsaron a cewarsa ta fi ta’azzara a Borno da kuma Yobe.

Ya ce rikici musamman tsakanin makiyaya da manoma ya yi sau?i a Benue da Nassarawa da Plateau da kuma Adamawa.

Tattalin Arzikin ?asa

A cewar Garba Shehu, farfa?owar tattalin arziki abu ne da ba zai faru ba a lokaci ?aya inda ya ce “abu ne da ba za a tashi yau a ce an wayi gari duk wanda ba shi da komai ya tashi aljihunsa cike da ku?i ya warware ba.”
Ya ce abin da ya kamata a mayar da hankali a kai shi ne irin matakan da gwamnati take ?auka don ganin cewa ta tada koma?ar tattalin arzikin ?asar.

“Shugaba Muhammadu Buhari ya za?i noma, ya za?i harkar ha?o ma’adinai wanda jama’a miliyoyi suke ta shiga yanzu suna ta yi,”
“Wadanda suka rungumi harkar noma yanzu a Najeriya ba wanda yake da-na-sani musamman harkar shinkafar nan, yanzu an shiga alkama, auduga, an shiga man kwakwa,”

“Haka da ?ai-?ai da ?ai-?ai ake ta bi ana ta tura ku?i da bashi mai sau?i ga wa?anda suke son su yi wa?an nan sana’oi kuma ana ganin suna samun ci gaba a rayuwarsu.” kamar yadda mai magana da yawun shugaban Najeriyar ya bayyana.

Sai dai Garba Shehu ya yi watsi da zargin cewa ‘yan siyasa na kashe mu raba da basukan da gwamnati ke bayarwa inda ya ce “suma ‘yan siyasa ai ‘yan Najeriya ne, amma abin ya fi ?arfin ‘yan siyasa nawa suke a cikin wannan al’uma ta mu,”

“Ana maganar cewa kamar manoman shinkafa sababbi wajen miliyan 12 suka shiga cikin wannan harka.”

Exit mobile version