Buhari Ya Yaba Ayyukan Mu – Shugaban ‘Yan Sanda

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaba Buhari ya yabawa shugabannin tsaro a wurin taronsu na jiya amma ya umarce su da su ƙara zage dantse domin kawo karshe matsalar tsaro baki ɗaya.

Sufeto Janar na rundunar yan sandan ƙasar nan, Usman Baba, Shine ya faɗi haka bayan ya halarci taron tsaro da ya gudanar a fadar shugaban ƙasa, Abuja, ranar Talata.

Da yake zantawa da manema labarai na gidan gwamnati, Usman Baba, yace Buhari ya umarci su ninka kokarin da suke domin kawo karshen kalubalen tsaron da ya addabi Najeriya.

A cewar shugaba Buhari sai an samu ingantaccen tsaro sannan yan Najeriya zasu samu damar cigaba da rayuwarsu kamar yadda suka saba.

Wane umarni Buhari ya sake baiwa shugabannin tsaro?

Sufeta Janar yace: “Mun tattauna a wurin taron tsaro, hafsoshin tsaro da shugabannin ɓangaren fasaha sun yiwa Buhari bayani kan halin tsaron da ake ciki a ƙasa.” “Shugaban ƙasa ya yi nazari sannan ya yi jawabin cewa doka ta ɗorawa gwamnati alhakin samar da tsaro ga yan ƙasa, kuma a shirye yake ya yi duk abinda ya dace.”

“Ya umarci mu kara zage dantse a kokarin da muke domin yana haifar da ɗa mai ido a arewa maso gabas, da Kudu maso gabas, amma da sauran aiki a arewa ta tsakiya da arewa ta yamma, inda mutane suke kokawa.”

Sufetan yan sandan ya bayyana cewa shugabannin tsaro sun tabbatarwa Buhari cewa zasu ninka kokarin da suke yi domin baiwa mara ɗa kunya. “Buhari ya gode mana kuma ya yaba mana kan kokarin da muka yi zuwa yanzun, sai dai ya bukaci mu kara akan da domin mutane su samu damar fita kasuwancin su yadda ya kamata.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply