Buhari Ya Umarci A Yi Wa Sarakuna Da Malaman Addini Riga-kafin CORONA

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce yana so Sarakuna da Limamai, manyan fastoci, manyan mawaka da yan wasanni a kasar su karbi allurar rigakafin korona kai tsaye a akwatin talbijin.

Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi na jihar Ekiti, ya bayyana hakan ga manema labarai a fadar Shugaban kasa bayan ganawa da shugabannin Najeriya a ranar Juma’a, 8 ga watan Janairu a Abuja.

A cewar wani rahoto daga jaridar Daily Sun, Gwamna Fayemi ya ce shugaba Buhari na so kwamitin fadar shugaban kasa kan korona ya kara manyan yan Najeriya cikin jerin wadanda za su karbi rigakafin kai tsaye a akwatin talbijin.

Shirin Allurar Rigakafin CORONA dai na cigaba da tayar da ƙura a tsakanin jama’ar Najeriya, tun bayan wata sanarwa da masana suka bayar na cewar allurar na da illa ga ‘yan Najeriya.

Labarai Makamanta