Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya taya zaɓaɓɓen Shugaban ƙasar Amurka Joe Biden murna kan zabensa a matsayin sabon shugaban Amurka ƙarƙashin jam’iyyar Democrats.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Twitter a daren ranar Asabar Shugaban ƙasa Buhari ya yi kira ga Mista Biden “ya kara kusantar kasashen Afirka bisa girmama juna da batutuwan da juna za su amfana.”
Da ya ke magana kan alakar kasa da kasa, Buhari ya bukaci zababben shugaban kasar ya yi amfani da kwarewarsa wurin magance mummunan siyasar son kai na kawai a siyasar duniya da ya janyo rarrabuwar kawuna.”
“Nasarar ka darasi ne da ke tunatar da mu cewa demokradiyya ce tsarin gwamnati mafi kyau don tana bawa mutane damar canja gwamnati cikin lumana,” in ji Buhari.
Har wa yau, Buhari ya ce yana fatan samun ganin hadin kai tsakanin Najeriya da Amurka musamman bangarorin tattalin arziki, diflomasiyya, siyasa da tsaro.
Sauran shugabanni kasashen duniya suma sun bi sahun Buhari wurin mika sakon taya murna ga Mista Biden.
Cikin wadanda suka mika sakon taya murnar akwai shugabannin kasashen Ireland, Canada, Birtaniya, Faransa da Jamus. Sauran su ne Greece, Belgium da Tarayyar kasashen Turai.