Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya sabon Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, murnar samun sarautar Zazzau. Shugaban kasar ya kara da shawartarsa da ya zama shugaba ga kowa da kowa.
Kamar yadda Malam Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasar, ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce wannan lokaci ne mai cike da kalubale. A don haka yayi kira ga Sarkin da ya yi amfani da wannan damar wurin hada kan dukkanin gidajen sarautar.
“Wannan lokaci ne mai cike da kalubale kuma ina yin amfani da wannan damar wurin kira gareka da ka yi amfani da ita wurin hada kan dukkan gidajen sarautar,”.
Daga bisani, shugaban kasan ya yi wa sabon Sarkin fatan hikima da kuma shiriyar Allah wurin sauke nauyin da ya hau kansa. “Ina fatan Allah ya baka hikima da kuma shiriya ta sauke wannan nauyin da ya hau kanka,”.