Buhari Ya Shirya Liyafa Ga Shugabannin Afirka

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis, 15 ga watan Oktoba, ya gayyaci Shugaban kasar Senegal, Macky Sall da takwaransa na kasar Guinea Bissau, Umaro Embalo zuwa wajen liyafar cin abincin dare a fadar Shugaban kasa da ke Abuja.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya tattaro cewa shugabannin yankin na Yammacin Afrika biyu sun kasance a Abuja bisa ziyarar aiki lokacin da Shugaban Najeriyan ya gayyace su taron cin abincin.

An ruwaito cewa Shugaban ma’aikatan fadar Shugaban kasar, Farfesa Ibrahim Gambari da wasu daga cikin mambobin majalisa da hadiman Shugaban kasar ma sun halarci taron.

Shugaba Buhari a ranar 21 ga watan Satumba, ya yi taro makamancin wannan tare da Shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo.

A gefe guda, mun ji cewa Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya karbi bakuncin tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan, wanda yakai masa ziyara domin gabatar masa da rahoto a kan rikicin kasar Mali.

Kazalika, Shugaba Buhari ya yi ganawar sirri da gwamnonin jihohin Arewa uku na jihar Kebbi, Atiku Bagudu, na jihar Jigawa, Badaru Abubakar, da na jihar Yobe, Mai Mala Buni.

Ya zuwa yanzu babu wani jawabi da fadar shugaban kasa ko gwamnonin suka fitar dangane da dalilin ganawarsu da Buhari.

Labarai Makamanta

Leave a Reply