Buhari Ya Rasa Dabarar Kawo ?arshen Matsalar Tsaro – Baba Ahmed

Dr Hakeem Baba Ahmed mai magana da yawun kungiyar dattawan arewa NEF, ya ce dabaru sun kare wa fadar shugaban kasa Baba-Ahmed ya ce takaici ke kama shi jin yadda a kullum fadar shugaban kasar ke naman bada uzuri a maimakon magance matsalar tsaro.


Kakakin NEF ya yi wannan jawabin ne yayin martani kan kalaman Garba Shehu mai magana da yawun shugaba Muhammadu Buhari.

Hakan ya biyo bayan maganar da Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa yayin tattaunawar da aka yi da shi ya ce jam’iyyar adawa na amfani da kallubalen da kasar ke ciki wurin sukar gwamnati. Ya ce wasu wadanda basu yi wa kasar fata nagari ne ke daukan nauyin tsirarun mutane da ke neman ballewa daga Nigeria domin ganin shugaban kasa ya yi kuskure. A martaninsa, Baba-Ahmed ya ce yanayin da Shehu ke magana na jefa shi cikin damuwa kuma yana tunanin dabaru sun kare wa fadar shugaban kasar. Kakakin na NEF ya ce yan Nigeria na son ganin an kawo karshen garkuwa da mutane ne ba wai bada uzuri ba.

Dr Hakeem ya ce ya gamsu da cewa dabaru sun kare wa fadar shugaban kasa, Baba Ahmed ya bayyana hakan ne yayin hirar da aka yi da shi a Channel Television a ranar Juma’a.

”Ya ce garkuwar ta bunkasa a karkashin gwamnatin Buhari kuma babu yadda zai musanta hakan duba da irin makaman da yan bindigan suka mallaka a yanzu. “Idan suna fuskantar babbar kallubale, sai su yi ta zagaye suna kame-kame na bada uzuri. Ba wannan yan Nigeria ke son ji ba. Muna so ne a kawo karshen garkuwa da mutane,” a cewar Baba-Ahmed cikin

Related posts

Leave a Comment