Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga sauran shugabannin nahiyar Afirka da cewar a haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen shawo kan matsalar tsaro da ke neman durƙusar da yankin baki ɗaya.
“Yanzu ta’addanci ya zama kamar wata muguwar cuta wacce za ta iya yaduwa a kowane lokaci matukar ba a dauki mataki na bai daya ba.”
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya fitar ranar Lahadi don mayar da martani kan kisan mutane 70 a garin Zaroumdareye, wani garin kan iyaka tsakanin Jamhuriyar Nijar da Mali da ‘yan bindiga suka yi a ƙarshen mako.
Shugaban wanda ya yi Allah wadai da lamarin tare da nuna damuwarsa ga yadda tsaro yake qara tabarbarewa, ya ce wannan wani karin kira ne na daukar matakin bai daya na shugabannin Afirka kan ta’addanci.
Shugaban ya ce: “Na yi matukar kaduwa da yawan mutuwar mutane marasa laifi a hannun wadannan mayaka marasa imani wadanda ba su kula da tsarkin rayuwar dan Adam.”
“Muna fuskantar babban kalubale na tsaro saboda mummunan yakin da ake yi na tashin hankali ba gaira ba dalili daga ‘yan ta’adda a yankin Sahel kuma hada kai kawai ne zai iya taimaka mana mu kayar da wadannan mugayen makiya na bil’adama.”
Shugaba Buhari ya ce “rashin zaman lafiya a wani yanki na Afirka na da tasiri ga tsaron wasu.” Ya tunatar da cewa “Tabarbarewar zaman lafiya a Libya a shekara ta 2011 yana haifar da matsala mai tasiri ga tsaron wasu kasashen Afirka da suka hada da Najeriya, Nijar, Chadi, Kamaru da sauransu.
Shugaban ya kara da cewa: “Satar kayayyakin makamai na Libya a bayan faduwar Gaddafi ya sanya muggan makamai a hannun ‘yan ta’adda da sauran masu laifi wadanda a yanzu suke haifar da kalubalen tsaro ga wasu kasashen.”
“Mun hadu ne da kaddara daya don haka dole ne mu hada kai mu hada karfi da karfe mu kawar da wadannan mugayen mutane da ke addabar mutanen da ba su ji ba su gani ba.
Shugaba Buhari ya ce “Bari na yi amfani da wannan damar don nuna matukar damuwata ga gwamnati, mutanen Nijar da dangin wadanda abin ya shafa.”