Buhari Ya Kashe Najeriya Da Bashi – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyar APC da su ba wa ‘yan Najeriya hakuri saboda nauyin bashin da suka tara wa kasar.

Atiku ya ce kamata ya yi gwamnatin Buhari ta amince da laifin jefa kasar nan cikin bashi mai nauyin gaske.

Furucin tsohon mataimakin shugaban kasar ya zo ne a yayin da ya ke babatu dangane da koma bayan ci gaba da kasar nan za ta fuskanta sakamakon kantar bashi.

Atiku ya ce, “Najeriya na da jimillar bashin ketare na dala biliyan 7.02 a ranar 29 ga Mayun 2015. Amma a yau, bashin mu na kasashen waje ya kai dala biliyan 23 kuma yana ci gaba da karuwa.”

Sai dai jam’iyyar APC yayin mayar da martani, ta ce tsohon mataimakin shugaban kasar ba ya da cancantar shigar da wannan bukata.

Jam’iyyar APC ta bakin kakakinta Yekini Nabena, ta ce Atiku shi ne ya cancanci ya bai wa ‘yan Najeriya hakuri kan basussukan da ya karbo a bankuna kuma har yanzu ya gaza biya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply